Shi dai itace ruman a turance ana kiran sa Pomegranate , kuma ya samo wannan suna ne daga sunan sa larabci wato

Rumman, inda Allah madaukakin sarki ya ambace sa a wurare daban-daban a cikin ayoyin sa na Al-Qur'ani mai girma.

Ruman

A sakamakon haka ne, wannan dan itace ya kasance daya daga cikin 'ya'yan itace masu matuƙar muhimmacin a duniya, domin kuwa Allah ya ambace shi a cikin aya guda tare da itacen zaitun, inda ya ƙunshi tarin sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam.

Wannan dan itace ya ƙunshi sunadarai da suka hadar da; Fiber, Protein, vitamin C, vitamin K, Folate da kuma Potassium.

Legit.ng ta kawo muku jerin cututtakan da dan itace ruman ke magancewa a sakamakon arzikin wannan sunadarai da ya ƙunsa:

1. Ciwon Zuciya.
2. Ciwon daji (musamman na mama, maraina da kuma mahaifa).
3. Rage teɓa da nauyin jiki.
4. Ciwon Sukari.
5. Hawan jini.
6. Cututtukan rashin ƙarfin mazakuta.
7. Kumburin jiki da ciwon gaɓɓai.
8. Cutar hauka da mantuwa.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top