Wani lokaci ba a iya gane matalar soyayya, musammam ma idan masoyan suna kaunar junar su. 

Lokacin da masoya suke son auren junansu, su kan iya zama kamar wadanda aka yi wa asiri ta yarda za ka ga ba su ji ba su gani ga duk wata alama daka iya kawo musu wata matsala bayan aure.

Da yawan mutane suna ganin Cewa bai dace ba ga masu son junansu da aure su dunga bi biyan laifuffukan abokin auren, musamman ma lokacin da suke gina soyayya a tsakaninsu.

 Hakan zai iya zama gaskiya, sai dai ya kamata mu kula da wadanda muke so da aure don kiyayewa da matsalolin da ka iya afkuwa kafun wakanar auren. 

Kawar da kai ga alamun da ka iya ba aurenka ko aurenki matsaloli, to lallai yin hakan baka ko baki cutar da kowa ba face rashin adalci ga kanka ko kanki. Akwai Alamu da dama da suke nuna cewa aurenki ko aurenka da wane ko wacce ba zai samu nasara ba.

 Duk da cewa alamun ka iya daukar lokaci kafin su bayyana amma dai bai dace a kauda kai a kan su ba lokacin da suka bayyana.


Akwai wasu abubuwa da ya kamata ma’aurata su kula kafin aure kamar haka:

Zamantakewa Da Sauran Mutane: Ya masoya suke gudanar da zamantakewa ga sauran mutane: Lalle dole masoya su kula da yana yin zamantakewar juna da rauran mutane kafin su yi aure. Masoya su duba junan su ta yadda za a kula da irin zamantakewan da yake gudana ga kowannan su, domin kaucewa matsaloli idan aka yi aure.

Rashin Girmama Iyakokin Masoyiya: Kusan dukkan mu, muna da wuraren da muke kiyaye wa, kuma yin hakan ba matsala bace. Shi kiyaye Iyakoki wata hanya ce da ke nuna cewa muna cikin zaman lafiya kuma muna da iko kan kula da makomarmu. Da yawan mutane suna son su bar abubuwan su a asirce babu wanda ya sani sai su kansu, kamar irin rayuwar cikin gida ko ta aiki, ko kuma abin da ya sa ba su jin dadin shiga cikin taron jama’a da dai sauransu. Lallai yana daukar lokaci kafin wani ya samu mazauni cikin zuciyar wani. In ya zamanto mutane suna ta yawan son tambayar ki a kan abin da ba ki san magana a kan shi, to ai hakan yana nuna cewan ba a girmama Iyakokin ki ba.

Karya: karya babbar matsala ce da yawan mutane suke kawar da kai a kan ta kafin aure. Lalle karya ita ce tushen matsaloli da ke afkuwa cikin auratayya. Mafi babban matsalolin da ma’aurata ke kau da kai a kan su ita ce karya.

Kin Bayyanarwa: Mutane suna kin bayyanar da kansu in ba su so su bayyanar da hakikanin zamantakewarsu da abokan zaman su.

Rashin yarda: Masoyan da suka nuna rashin yarda a tsakaninsu kafin aure, akwai yiwuwar su ki yarda da kansu bayan aure. Rashin yarda na da alaka ne da yin karya. Lokacin da ka ke tare da wanda bai da gaskiya, to akwai yiwuwan rashin yarda. Irin wannan dabi’a, tana daya daga cikin manyan matsalolin da ya dace ake an lura da su kafin aure. Lokacin da mutum yake cikin tsan-tsar soyayya, za ka ga yana gaya wa mutane cewa, wacce ita ce masoyiyata ko wane shi ne masoyina.

Yawan Korafi: Yawan korafin yana zama babban matsala ga auratayya, domin za a iya ce maka baka kulawa da matarka idan kana yawan kai korafin ta. Ko ma dai wace irin hanya aka dauka, dukkan su matsaloline wadanda bai dace akwau da kai a kan su ba kafin aure.

Al’adun: In al’adun masoya suka zama daban-daban kuma kowa ba zai iya hakura da na shi ba, to lallai za a samu yawan korafi ko rashin fahimta a tsakanin ku. Wadannan banbance-banbancen sun dace a tattauna a kan su kafin shiga cikin soyayya mai zarfi. Wannan ba a bin da zai canzu ba ne cikin sauki, to in kuka kau da kai a kan irin wannan matsala, to ku za ku shiga cikin matsala babba. In har ba ka yarda da mutum ba, to tun wuri a rabu ba sai an yi nisa cikin soyayya ba.

Ba Su Farin Ciki Da Kansu: kamar dai ka ga mutane sun zauna da rayuwarsu a wuri daya, amma ba sa farin ciki da kansu, yin hakan yana haifar matsaloli. Mutane ba za su iya zama cikin rayuwar farin ciki su kadai ba, dole da farko sai sun zama masu farin ciki da junansu kafin su yi aure. In ba ku farin ciki da junan ku, dole sai wata rana an rabu kuma da bacin rai. To a irin haka, abun da ya fi dacewa a lura da shi kafin aure

Sun Nuna Ba su Da Damuwa Ga Muradunka: Lalle zamantakewa ba ta daurewa har idan babu girmama muradunka, ra’yinka da tunaninka a kan komai. Duk irin wannan halayya ta rashin girmama muradunka, ra’ayunka da kuma tunaninka, to ba abin da zai biyo baya sai matsala. In Abokin zamanka ko zamanki baya mutunta muradunki ko muradunka, to lallai ya dace ka nemi wani daban wanda zai damu da su.

Ko Da Yaushe Zargin Wasu, Baka Yarda Da Matsalarka:

 Akwai babbar matsala in har ba za ka amsa kuskure ba ko kuma dai kullum sai zargin wasu a kan kuskuren su, to za a samu matsala babba wajen zamantakewar aure. Lalle dole ma’aurata su kula da kasalanci da datti a bangaren abokin aure.

Abu me sauki ne muka ba uzuri ga wanda muka fadawa soyayya, to ai ashe burgewace mu lura da wadannna alamu kafin mu yanke shawarar afkawa aure ta yadda za mu yi zamantakewa cikin kwanciyar hankali.

 Idan muka lura da wadannan abuwa, to lallai za mu samu zamantakewar aure wacce ba ta da kura a cikin ta. Kar mu bari soyayya yana dauke mana hankali ta yadda ba za mu iya kula da wadannan abubuwa ba. Allah ya ba mu ikon lura da wannan abubuwa kafin mu yi aure.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top