Suna: Miskila.
Tsara labari: Yusuf DanKundalo
Kamfani: Dan Hajiya Film Production
Daukar Nauyi: Shamsi Dan Iya
Shiryawa: Naziru Dan Hajiya
Bada Umarni: Hussaini Ali Muhammad.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad
Jarumai: Shehu Hassan Kano, Hadiza Muhammad, Ali Nuhu, Maryam Danko, Hassana Muhammad, Sukhairaju Yusuf, Hauwa Kabir, Gwaggo Duduwa, Yusuf Muhammad Abdullahi da sauransu.

Fim din ‘Miskila’ labara ne na wani Attajiri Alhaji Kabir (Shehu Hassan Kano) wanda ya kasance mai tsananin kaunarwata ‘yarsa Nana (Hassana Muhammad) wadda ya fifita soyayyarta akan ta kowa acikin gidansa. Wannan soyayyar daya ke yi wa Nana ta samu ne sakamakon rashin mahaifiyarta da ta yi tun lokacin data haifeta. Hakan ne ya saya sakamata sunan mahaifiyarsa, yake kiran tadamomi yayin da sauran ‘yan gida suke kiranta da Nana. Wannan fifikon soyayya da Alhaji yake nuna wa Nana, ita ce ta saka bata ganin mutuncin kowa a cikin wannan gida, kuma wannnan halin a rashin ganin mutuncin mutane shi ne ya bi ta har gidanta bayan ta yi aure ta auri Habib (Ali Nuhu), wanda har saki daya kai yasa kota, amma daga baya aka yi musu sulhu ya maida ita.
A dayan bangaren kuma, Alhaji yan adamata mai suna Hajiya Zulai (Hadiza Muhammad) wadda take da’ ya’ya biyu: Nasir (Sukhairaju Yusuf) da kuma Husna (Maryam Danko). Hajiya Zulaida‘ ya’yanta basa jin dadin zaman gidansu sakamakon halin ko-in-kulada Alhaji Kabir yake nuna musu, ko kadan baya shiga lamarinsu. Babu abin da yake hada shi dasu kullum sai tsangwama, fada, kyaradacin- mutunci. A haka suka kasance cikin rayuwa mai cike dakunci da takaici duk da kasancewar su a gidan mai arziki. Ana ta bangaren, Hajiya Zulai kullum bata da aiki sai yi wa’ ya’yan tana siha cewa suka sance masu hakuri akan duk irin abin da mahaifinsu yake musu, tana fada musu su kasance masu hakuri, domin komai mai wucewa ne.
A haka dai akaci-gaba da wannan rayuwa a cikin gidan Alhaji. Husna tasa musaukin halin ko-in-kula da mahaifinsu yake nuna musu tun bayan lokacin data yi aure, kuma tayi dace da miji na gari wanda harya saya mata motar hawa kuma ya biya mata kudi domin suje yawan shakatawa a kasashen duniya.

A karshen labarin, Alhaji ya gane kuskurensa, wanda hakan yasa ya tara ahalinsa ya basu
Hakuri sannan ya yi alkawarin basu cikakkiyar kulawa a matsayinsu na iyalansa. Ita ma Nana ta yi nadamar munanan dabi’unta na miskilanci. Ta nemi afuwar wadanda ta ringa wulakantawa abaya, sannan tazo ta nemi afuwar Hajiya a gida da kuma yayanta Nasir.
Abubuwan Yabawa
1. Sunan shirin ya dace da labarin, duba da irin yadda Nana ta rinka nuna halin miskilanci a gidansu da kuma gidan mijinta.
2. Labarin ya samu nasarar rike mai kallo tun daga farkonsa har karshensa ba tare da labarin ya karye ba.
3. Sauti ya fita radau, haka daukar hotuna ma abun a yaba ne.
4. Jaruman da aka saka a fim din sun dace da labarin duba da irin rawar da suka taka a cikin shirin.
5. Bayyanar nadamar Alhaji Kabir da Nana a karshen labarin, zai zama izina ga masu yin dabi ’u irin nasu.

KURAKURAI

1. An samu sabani tsakanin hotuna da furuci na kusan mintina 9, yayin da furucin yakan riga motsawar bakin masu furucin.
2. Har kusan mintina 40 ba a nuno Alhaji tare da iyalansa ba, duk da cewa a gida daya suke rayuwa, musamman matarsa Hajiya Zulai wanda hakan ya sabawa yanayin zamantakewa na iyali.

3. A cikin labarin an nuna cewa, Alhaji Kabir yana yawan zargin cewa, Hajiya Zulai da ‘ya‘yanta suna takurawa Nana a cikin gida wanda hakan yasa ya fifita soyayyarta akan tasu, amma kuma ko sau daya ba a nunosu tare a cikin gidan ba, balle mai kallo ya gasgatasu na takura matanne ko a a.

4. A fitowar da Alhaji yake yi wa Hajiya fada saboda taje gidan Nana ta bata shawara akan ta gyara munanan dabiunta, an jiyo muryar Alhaji yanata yi wa Hajiya fada tsawon minti 1 da dakika 49 ba tare da an hasko hotonsa ba a yayin da yake yi mata fadan.
5. Ya kamata a nuna Nana tana bayyana nadamarta ga mijinta Habib duba da irin wulakancin da ta rinka yi masa a gidansa.

KARKAREWA

Fim din MISKILA fim ne mai cike dada rusa da dama. Ya nuna mahimmancin hakuri da kuma irin ribar da mai yinsa yake samu, kamar yadda ya faru akan Hajiya Zulaida ’yarta Husna. Sannan ya nuna illar nunawa ’ya’ya gata fiye da tunani wanda hakan yakan zama silar samun rashin ingantacciyar tarbiya a gurinsu kamar yadda ya faru da Nana. A takaice, wannan fim yasa mu nasarori da dama duba da dacewar labarin da fim din. Haka kuma, yana da kyau masu ruwa-da-tsaki su rinka lura sosai kafun a saki fim, a rinka kulada wasu matsaloli da kai ya rage kwar jinin fim din.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top