Bismillahi wassalatu wassalam ala rasulillah s.a.w.
Itaciyar magarya wadda akafisani da (Assidir) a larabce itaciyace mai albarka da daddeden tarihi, Tunkafin zuwan musulinci ana amfani dashi kuma bayan zuwan musulinci Annabi s.a.w ya tabbatar da amfaninsa duk da su turawan yamma sai afarkon karni na shatara suka sanshi.

Magarya yana kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma yana da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci magarya Antibiotic ne mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato side effects na azo agani.

KADAN DAGA CIKIN AMFANINTA:

1. Ciwon daji (cancer) : Idan ana
dafa garin magarya anasha da
zuma yana kashe kwayar cutar
daji koda nacikin jini ne idan
kuma Yayi miki sai arinka dafa
garin magaryar da ruwan khal
ana wanke wurin mikin idan an
wanke sai a barbada
garin magaryar.

2. Yanada karfin yaqar cutar
fata kamar su tautau, makero,
Kanzuwa da sauransu sai
A kwaba shi da zuma
arinkasha Ana shafawa a
Wurin da abin ya shafa.

3. Yana tsaftace jini domin
Yana dauke da sinadarin
Saponin,alkaloid da
triterpenoid wadannan
Sinadaraine masu tsaftace
Jini.

4. Shansa da ruwan zafi yana
magance gajiya da ciwon
Jiki.

5. Yana magance ulcer idan
ana shansa da madara ko
zuma.

6. Yana taimakawa hanta ya
hanashi jin ciwo da
cututtuka.

7. Yana daidaita nauyin
mutun.

8. Yana tsaida zawo cikin
kankanin lokaci idan aka
Shashi da ruwa ko koko.

9. Yana miqar da kasusuwa
musamman ga mai karaya.

10. Yana maganin rashin shaawa ga mata idan
suna tsarki dashi kuma Suna shansa da
madara. 

Wallahu Alalam.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top