Shahararren malamin addinin musuluncin nan Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya jaddada bukatar 'yan siyasa dole ne su dinga girmama sarakunan gargajiya - Malamin ya fadi hakan, inda ya bayyana cewa dole ne mu dauke sarakuna a matsayin iyaye Shahararren malamin addinin musuluncin nan kuma, jigo a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, a wata hira da jaridar Aminiya ta yi da shi, ya jaddada bukatar 'yan siyasa suke girmama sarakunan gargajiya, inda ya kawo dalilai masu yawa.

 Ga yadda hirar ta su ta kasance.

 Aminiya: Yawancin 'yan siyasa sun yadda cewa sarakunan gargajiya sun baci da shiga sabgar siyasa. Shin, kana tsammanin maganar ta su akwai kanshin gaskiya a cikinta?

Pantami: Kowane dan Najeriya yana da ikon yin maganar da yaga dama idan aka zo ta fannin shugabanci. Duk da haka, na sha jin irin wadannan zarge-zarge akan sarakunan mu na gargajiya.

Misali yanzu idan wani yazo gurina, kuma ina jin kunyar shi mutuka, har na yabe shi. Sai kaga wasu wadanda basa son wannan mutumin sun fito suna cewa na goya mishi baya. Yabon mutum ba shine yake nuna cewa kana goyon bayanshi ba. 'Yan siyasa suna zuwa gurin sarakunan mu na gargajiya, kuma suna karbar su hannu biyu-biyu. Fada mini wani Sarki a kasar nan da ya ki karbar ziyarar dan siyasa a kasar nan, ban tunanin akwai.

 Aminiya: Ka ambaci wasu fannoni da ke nuna cewar sarakunan suna da muhimmanci, amma a wadanne hanyoyi ne kake ganin cewa sarakunan gargajiya za su taimaka wurin magance matsalolin cikin al'umma?

Pantami: Yawancin masarautun gargajiyan mu na Arewa, sun samo asali ne tun lokacin Shehu Mujaddadi Dan Fodio, an kafa su akan turbar addini, kuma addini shine ginshikin rayuwarmu. Sannan kuma sune kashin bayan dukkanin al'adunmu. Kuma dukkanin mu muna girmama al'adun mu.

Bayan haka, daga shekarar 1804 a lokacin da aka kashe Sultan Attahiru a Burmi, bayan ya bar Sokoto zai je aikin Hajji, an yi watsi da al'adu da sarakunan gargajiya, a wasu wuraren ma har an daina amfani da su. Dole ne mu tabbatar da cewa muna girmama su, kuma hakan ya hada da malaman addini, ma'aikatan gwamnati, gwamnoni, da duk wasu masu mukami, kai har ma da wadanda ba su da mukamin komai.

Bisa ga matsayin da suke dashi, bai kamata mu dubi yawan shekarunsu ko wata halayya ta su ba, kamata yayi muna girmama su, mu dauke su a matsayin iyaye a garemu, saboda ba a bai wa malaman addini da sarakunan gargajiya girma saboda yawan shekaru, amma ana basu girma saboda wakilcin da suke dashi a kansu.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top