RABA MASARAUTAR KANO

Fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya magantu akan rikicin da ya barke tsakanin tsagin gwamnati da masarautar jihar Kano.

Sheikh Bauchi ya magantu da cewa lallai abinda ya faru a Kano na raba masarauta, abin tsoro ne ga mutane, domin ita jihar Kano, jiha ce ba gama garin jihohi ba.

“Abin da ya faru a Kano ya tsoratar da mutane, Bature ya ci kasar nan (Nijeriya), ya mallaki kasar, har ya gama shegantakar shi da shekara 60 bai taba masarautar Kano da sunan wargazawa ba.”

Sheik Dahiru Bauchi yace tin sanda aka fara mulki a jihar Kano da Najeriya, Sarakuna da masu mulkin siyasa, babu wanda yayi wa Kano abinda ake mata yanzu ba.

“Wadanda suka yi sarauta da mulki, an yi gwamnati wajen kusan gwamnati 9 na sojoji, 7 na fafar hula a Kano, amma ba wanda ya tunkari Kano da irin wannan abinda ake tunkartar a yi yanzu, domin Kano ba irin sauran jihohi bace, zan nanata".

Sheik ya kara da cewa, ya yi niyyar yiwa mutanen jihar Kano jajen abinda ya faru, amma bayan ya samu labarin ruguje Sarakunan da Kotu tayi, yayi farin ciki da jin lamarin.
Rariya.

Post a Comment

 
Top