A yau ne babban chinedu ya fitar da wata budadiyyar wasika zuwa ga gwamna ganduje akan zargin Ismail na abba Afakallahu ya ci kudin marayu wato iyalan Margayi Ibro.



Shine shikuma baiyi wata wata ba ya maka shi kotu domin a can ne kawai yake ganin mai girma zai daukar girmansa.

Ga rubutun da shafin kannywood exclusive na Wallafa a shafin su

"LAUYOYI SUN UMARCI BABAN CHINEDU YA BA AFAKALLAHU HAKURI.
A jiya ne Jarumin Finafinan Hausa kuma mawaki Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu, ya zargi Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano Isma'il Na'Abba Afakallahu da cin kudin Marayu.

A bidiyon Baban Chinedu ya ce, ya yi bincike na musamman daga majiya mai tushe inda ya tabbatar da cewa Ganduje ya biya kudi kimanin naira miliyan 5, domin a sayawa diyar marigayi Ibro kayan daki a lokacin auren ta, amma Afakallahu buhun shinkafa 2, da naira dubu 20 sai mai, kawai  ya kai wa iyalan Mamacin.

Haka zalika a cikin maganganun sa ya yi kira ga Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya tura wakilan sa gidan marigayi Ibro domin bincika sahihancin maganar sa. A cewar sa, idan har aka gano Afakallahu ya ci kudin nan, yana kira da a sauke shi daga mukamin sa domin mai irin halin sa bai cancanci zama shugaba ba.

Bugu da kari Baban Chinedu ya sake yin kira na musamman ga malaman Kano da subi kadin zancen sa sannan su bi wa 'ya'yan ibro hakkin su.

Daga karshe kuma ya kalubalanci Afakallahu da ya fito kafafen watsa labarai ya kare kan sa, idan kuma karya ya ke yi masa a kama shi, idan kuma aka yi shiru ba a kai shi kotu ba, zai ci gaba da yayata wannan maganar, in ji Baban Chinedu.

Sai dai kwatsam a yammacin yau Talata, 18 ga watan Fabrairu 2020, sai aka ci karo da wata takarda da Afakallahu ya wallafa a shafin sa na Instagram. 
Inda ya umarci lauyoyinsa da su shigo cikin lamarin bata masa suna da Baban Chinedu yay

Lauya Abdullahi Musa Karaye, tare da abokan aikin sa lauyoyin da ke kare Afakallahu sun umarci Baban Chinedu ya sauke bidiyon da ya saka a dukkan shafukansa sannan ya sake yin wani bidiyon na bayar da hakuri tare da karyata kan sa a cikin awa 24.

Idan wa'adin ya cika ba tare da yayi hakan ba, za su garzaya zuwa kotu domin nemawa Afakallahu hakkinsa akan wannan bata suna da Baban Chinedu ya yi. © Kannywood Exclusive
18-02-2020"

Ga dai abinda ya wallafa a shafinsa na instagram.



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top