Maryam CTV, ta tabbatar da hakan ne a lokacin da su ke tattaunawa da wakilin mu dangane da halin da masana'antar ta tsinci kanta a ciki.
Ta kuma fara da cewar "To harkar fim dai ga ta nan ba a ce ba a yi ba, sai dai ba kamar yadda a ka saba yin ta a baya ba, domin ka san da kakar siyasa ta zo, sai 'yan fim mu ka tafi harkokin siyasa, to da a ka gama ne sai wasu su ka ci gaba da harkokin su na kasuwanci, wasu kuma su ka koma harkar gona, saboda halin da harkar fim din ta ke ciki, domin haka sai kowa ya tafi ya nemawa wa kan sa mafita, ka ga halin da a ke ciki a yanzu".
Mun tambaye ta a matsayin ta na uwa a cikin harkar, ko ya ya ta ke ganin irin matsalolin da su ke faruwa a cikin harkar wanda a ke danganta su da matan cikin masana’antar?
"To gaskiya hakan ta na faruwa, amma ba abu ne da mu ke jin dadin sa ba, kuma muna ta kokari domin kawo gyara. Sai dai mutane su sa ni cewa, mu a karan kan mu kadai ba za mu iya kawo gyaran ba, sai kowa ya bayar da ta sa gudummawar, domin a samu canjin da a ke bukata. To Amma dai yanzu za a iya cewa an kamo hanyar gyaran, domin ko rijista da hukumar tace fina-finai ta Kano ta ke yi, to wannan hanya ce da za ta taimaka domin kawo gyara a cikin harkar, domin haka ka ga idan hukuma ta shigo cikin harkar, to sauran jama'a ma sais u kawo tasu abun da ya kamata kenan, to za a kawo gyaran, amma dai mu kadai ba za mu iya ba". Inji Maryam CTV
Daga karshe jarumar ta yi kira da jama'a da su rinka kyautata musu zato, domin duk dan Adam tara ya ke bai cika goma ba.
©HausaLoaded
Post a Comment