Jarumin Finafinan Hausa kuma mawaki Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu, ya zargi Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano Isma'il Na'Abba Afakallahu da cin kudin Marayu.

Baban Chinedu ya wallafa wani dogon bidiyo mai tsawon minti 8 da sakan 58 a shafin sa  na Instagram inda ya yi wa bidiyon ta ke da "Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Gwamnan Kano"

A cikin bidiyon ya bayyana godiyar sa ga Ganduje akan yadda ya dauki nauyin biyan kayan dakin amarya na babbar diyar Ibro wadda aka daurawa aure shekaru biyu da suka gabata.

Baban Chinedu ya ce, ya yi bincike na musamman daga majiya mai tushe inda ya tabbatar da cewa Ganduje ya biya kudi kimanin naira miliyan 5, domin a sayawa amarya kayan daki, amma Afakallahu buhun shinkafa 2, da naira dubu 20 sai mai kawai Afakallahu ya kai wa iyalan Ibro, bai kai masu kudin ba, kuma bai sai kayan ba.

Baban Chinedu ya ci gaba da cewa tun a lokacin ya yi iya bakin kokarin sa wajen bin shi  domin ya kai masu kudin nan amma ya kiya, ya kuma bayyana Falalu A. Dorayi a matsayin shaidar sa.

A cewar sa abin bakin ciki a kwanan nan, sai da iyalan marigayin suka sayar da gida sannan suka biya bashin wadancan kayan dakin da suka saya. Ya kuma ce nan bada dadewa ba za a sake yi wata daga cikin 'ya'yan ibro aure, sannan daman ya dauki alkawarin cewa idan har lokacin auren ya karato Afakallahu bai biya kudin ba ya sha alwashin fasa kwai.

Haka zalika a cikin maganganun sa ya yi kira ga Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya tura wakilan sa gidan marigayi Ibro domin bincika sahihancin maganar sa. A cewar sa, idan har aka gano Afakallahu ya ci kudin nan, yana kira da a sauke shi daga mukamin sa domin mai irin halin sa bai cancanci zama shugaba ba.

Bugu da kari Baban Chinedu ya sake yin kira na musamman ga malaman Kano da subi kadin zancen sa sannan su bi wa 'ya'yan ibro hakkin su.

Daga karshe kuma ya kalubalanci Afakallahu da ya fito kafafen watsa labarai ya kare kan sa, idan kuma karya ya ke yi masa a kama shi, idan kuma aka yi shiru ba a kai shi kotu ba, zai ci gaba da yayata wannan maganar, in ji Baban Chinedu.

Ga dai Bidiyon nan kuji Daga Bakinsa.






©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top