Wani yar tsama ta taso tsakanin jarumi adam a zango da hukumar tace fina fina shine wannan babban darakta ya fadi albarkacin bakinsa.
Hausaloaded.com sun samu wannan ne shafin daraktan falalu dorayi ga abinda yake cewa:-

"ADALCI
Idan har hukuma zata bawa film certificate a nuna shi a Cinema, duk da akwai Jarumai marasa register da hukuma a shirin, babu hujja hana jaruman cikin film zuwa su gana da fans dinsu. Idan akwai hujjar, zata fara ne daga lokacin da Film din yazo hannun hukumar, sai su hana certificate su ce wane bai register damu ba.

Abin da mamaki, nasan Jarumai da mawaka da dama da basu da lasisin hukumar suna halattar gurin nuna film a Filmhouse, wani film sune a ciki, wani kuma kallo kawai suka je, ba’a taba yinkurin kama su ba, sai rana tsaka ace an hana wani saboda bashi da lasisin hukuma.

Adalci shine ayi hukunci na bai daya babu nuna fifiko, menene bambancin sa da DIJA? Ba a kano take ba, ba a kano yake ba, idan har za’a barta tazo mai zai hana zango zuwa? Bana jin DIJA na da lasisin hukumar. Haka kuma Idan za’a bar wadancan Jarumai da mawaka marasa lasisin hukuma su zo kallo, Mai yasa aka hana zango?
Kungiya raayi ce, idan kaga abin da kungiya take baya gamsar da kai, kana da ikon fita, kuma ba kan zango aka fara fita daga kungiya ba. Adam A. Zango ya sanar ya fita daga kungiya, amma ba shine yake nuna ya daina zamunci da Kano ba. Mai yasa hukuma take kokarin mai da abin ya zama hada husuma, ni dai ban taba ji zango ya zagi ko cin zarafin kano ba. Kar muyi amfani da siyasa mu jefi Yan uwanmu da sharri.

Jagora nagari ana so niyyarsa ta zamo mai kyau bata san zuciya ba.
Sannan ya zamo mai yin abu domin Allah, ba domin a gani a fada ba. Kuma kar ya zamo mai aibata ko cin zarafin mutane.

Idan Jagora yana so wadanda yake jagoranta suyi masa biyayya, sai yai Jagoranci da adalci. Ya kiyaye nuna fifiko. Ya bawa dokar gaskiya dama tai aiki, ba dokar fadi a baki ba.
Jagora ya zamo mai aiki da mashawarta nagari, kar ya zamo mai mulki domin bukatar wasu, hakan shike kawo mulkin zalinci, har ta kai ana kin girmama juna.

Tunatarwa
Qurani a cikin An-Nisa’i (58)
Allahu (SWT) Yace;
“Lallai ne Allah yana umarnin ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.
KUMA IDAN ZAKU YI HUKUNCI TSAKANIN MUTANE, KUYI HUKUNCI DA ADALCI, LALLAI NE ALLAH MADALLA DA ABIN DA YAKE YI MUKU WA’AZI DA SHI.
LALLAI NE ALLAH YA KASANCE MAI JI NE, MAI GANI.”
#FalaluADorayi
#Baba"


View this post on Instagram

ADALCI Idan har hukuma zata bawa film certificate a nuna shi a Cinema, duk da akwai Jarumai marasa register da hukuma a shirin, babu hujja hana jaruman cikin film zuwa su gana da fans dinsu. Idan akwai hujjar, zata fara ne daga lokacin da Film din yazo hannun hukumar, sai su hana certificate su ce wane bai register damu ba. Abin da mamaki, nasan Jarumai da mawaka da dama da basu da lasisin hukumar suna halattar gurin nuna film a Filmhouse, wani film sune a ciki, wani kuma kallo kawai suka je, ba’a taba yinkurin kama su ba, sai rana tsaka ace an hana wani saboda bashi da lasisin hukuma. Adalci shine ayi hukunci na bai daya babu nuna fifiko, menene bambancin sa da DIJA? Ba a kano take ba, ba a kano yake ba, idan har za’a barta tazo mai zai hana zango zuwa? Bana jin DIJA na da lasisin hukumar. Haka kuma Idan za’a bar wadancan Jarumai da mawaka marasa lasisin hukuma su zo kallo, Mai yasa aka hana zango? Kungiya raayi ce, idan kaga abin da kungiya take baya gamsar da kai, kana da ikon fita, kuma ba kan zango aka fara fita daga kungiya ba. Adam A. Zango ya sanar ya fita daga kungiya, amma ba shine yake nuna ya daina zamunci da Kano ba. Mai yasa hukuma take kokarin mai da abin ya zama hada husuma, ni dai ban taba ji zango ya zagi ko cin zarafin kano ba. Kar muyi amfani da siyasa mu jefi Yan uwanmu da sharri. Jagora nagari ana so niyyarsa ta zamo mai kyau bata san zuciya ba. Sannan ya zamo mai yin abu domin Allah, ba domin a gani a fada ba. Kuma kar ya zamo mai aibata ko cin zarafin mutane. Idan Jagora yana so wadanda yake jagoranta suyi masa biyayya, sai yai Jagoranci da adalci. Ya kiyaye nuna fifiko. Ya bawa dokar gaskiya dama tai aiki, ba dokar fadi a baki ba. Jagora ya zamo mai aiki da mashawarta nagari, kar ya zamo mai mulki domin bukatar wasu, hakan shike kawo mulkin zalinci, har ta kai ana kin girmama juna. Tunatarwa Qurani a cikin An-Nisa’i (58) Allahu (SWT) Yace; “Lallai ne Allah yana umarnin ku bayar da amanoni zuwa ga masu su. KUMA IDAN ZAKU YI HUKUNCI TSAKANIN MUTANE, KUYI HUKUNCI DA ADALCI, LALLAI NE ALLAH MADALLA DA ABIN DA YAKE YI MUKU WA’AZI DA SHI. LALLAI NE ALLAH YA KASANCE MAI JI NE, MAI GANI.” #FalaluADorayi #Baba
A post shared by F A L A L U A. D O R A Y I (@falalu_a_dorayi) on


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top