WATA sabuwar 'yar wasa ta yi kira ga jama'a da su daina yi wa 'yan fim kallon bai-ɗaya har su na ɗauka cewa duk halin su ɗaya idan wani ya yi abin da bai dace ba.jaridar fim magazine na ruwaito.

Wadda ta yi wannan tsokacin wata ce mai suna Khadija Alhaji Shehu, wadda aka fi sani da Khadija Yobe.

Jarumar 'yar shekara 25 ta yi wannan kalami ne a lokacin da ta ke zantawa da mujallar Fim a Kano kwanan nan.

Ita dai Khadija Yobe, ana yi mata ganin ta shigo harkar fim da ƙafar dama domin kuwa duk da yake ba ta daɗe a ciki ba, amma ta samu shiga cikin manyan finafinai.

Hakan ya nuna cewar ita ma nan gaba kaɗan za ta iya shiga cikin sahun manyan jaruman da ake damawa da su.

Ba abin mamaki ba ne idan har hakan ta kasance, domin kuwa da ilimin ta Khadija ta shigo Kannywood. Ta na da digiri a fannin gudanarwa, wato 'Public Administration'. Don haka ana hangen ko me za ta yi sai ta auna shi.

A hirar ta da mujallar Fim, jarumar ta bayyana cewa ita asali Bafillatana ce daga garin Damaturu a Jihar Yobe. Amma haifaffiyar Maiduguri ce a Jihar Borno. Sai dai duk karatun ta a Damaturu ta yi shi.

Da mujallar Fim ta tambaye ta yadda aka yi ta samu kan ta a Kano kuma har ta shiga masana'antar finafinan Hausa, sai Khadija ta amsa: "To gaskiya garin Kano ni ba baƙuwa ba ce, domin lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani sai baban mu ya taso, mu ka dawo Kano. Sai da mu ka yi shekara huɗu, mu ka koma gida.

"To kuma da man mu na da 'yan'uwa da yawa a nan, don haka ko da na gama karatu na, na ji ina son na shiga harkar fim, sai na dawo na zauna a wajen 'yan'uwan mu.

"Don haka yanzu ina garin Kano da zama.

"Na zo masana'antar Kannywood ne domin ni ma na bada tawa gudunmawar, domin tun ina yarinya na ke so na yi fim, sai dai a lokacin ban samu dama ba."

Ko a wane fim ta fara fitowa, kuma zuwa yanzu finafinan da Khadija ta yi za su kai kamar nawa?

Amsa: "To da ya ke ban daɗe da shigowa ba, don a cikin wannan shekarar ta 2020 ma aka fara sa ni a fim, amma dai fim ɗin da na yi wanda aka gan ni a ciki shi ne 'Wutar Kara', sai kuma 'Hikima' wanda a yanzu mu na aikin sa, ba a kammala ba. Sai dai na fito a wasu finafinan da yawa, ban riƙe sunan su ba, da kuma waƙoƙi, waɗanda sai nan gaba za su fito."

Kowanne jarumi akeai burin da ya ke shigowa harkar fim da shi. To ita Khadija Yobe menene nata burin?

"Ni dai babban buri na shi ne faɗakarwa ga al'umma kamar yadda sauran jarumai su ke yi, domin na san harkar fim akwai faɗakarwa a cikin ta, don haka na zo na bayar da tawa gudunmawar."

Jarumar ta ce babu wata matsala da ta fuskanta wajen shigowar ta cikin harkar fim. "Gaskiya babu wata matsala da na fuskanta, domin baban mu ya na da fahimtar al'amura, don haka da na yi masa bayani, ya gamsu. Don haka da amincewar sa na shigo cikin harkar."

A game da maganar aure, Khadija ta ce ita ba ta taɓa yin aure ba.

Da Fim ta tambaye ta yadda ta ga al'amura su na gudana a cikin Kannywood, sai sabuwar jarumar ta ce, "Babu wata matsala, domin ni ban ga wani abu  ba kamar yadda ake ta faɗa.

"Sai dai mutane su gane, kowa da irin yadda ya ke gudanar da rayuwar sa - ko ɗan fim ko ba ɗan fim ba. Don haka bai kamata a rinƙa yi wa 'yan fim kuɗin goro a kan abin da aka ga wani ya yi ba."

A ƙarshe, Khadija Yobe ta miƙa saƙo ga 'yan'uwan ta 'yan fim, inda ta ce, "Ni dai ina kira ga 'yan fim da su haɗa kai domin sai da haɗin kai ne za a cimma nasara a kan abin da aka sa a gaba.

"Ina yi wa kowa fatan alheri. Allah ya ƙara haɗa kan mu."

To amin Khadija.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top