Daya daga cikin fitattun mawakan Hausa, Binta Labaran wacce aka fi sani da 'Fati Nijar' ta ce ta kusa ta saki wani sabon albom mai dauke da sabbin wakokinta shida a ciki.
Fati dai ta dade tana jan zarenta a fagen waka a harkar fina-finai da wakokin Hausa na Kannywood.
A cikin wata hira ta musamman da ta yi da BBC Hausa, Fati, wadda 'yar asalin Jamhuriyar Nijar ce, ta yi bayanai da dama kan rayuwarta da ma yadda aka yi ta fara waka a Najeriya.
Baya ga wakoki da take yi a fina-finan Kannywood da bukukuwa, tana yin wakoki har ga masu rike da mukamman gargajiya da attajirai.
Ga dai yadda tattaunawar tasu da mukaddashin shugaban sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko ta kasance:
Wannan layi ne
Aliyu Tanko: Me ya sa kika shiga waka?
Fati Nijar:Wai! kusan gaskiya zan iya cewa ni tun da na taso ban ma taso da sha'awar yin waka ba. To zuwa na Najeriya dai Allah ya sa waka ce abincina kuma har Allah ya sa na shiga aka sanni a duniya, Alhamdulillah.
Aliyu Tanko:Kin gaji waka ne ko kuwa haka kika fara kai tsaye?
Fati Nijar:Gaskiya ban gaji waka ba kuma ban ma taba tunanin zan yi waka ba gaskiya. Ban gaji waka ba haka kawai na soma, kuma Allah Ya sa da abincina a ciki kuma za a sanni a kan hakan.
Aliyu Tanko:To kamar ya aka yi kika gano kina da baiwar yin waka?
Fati Nijar:Eh to gaskiya da yake ka san yawanci mutum ba a gane yana da wata baiwa sai an gwada shi.
Ni dai daga farko dai daga gwaji ne aka fara, a haka har na gano zan iya waka, tun da lokacin da na zo Najeriya na zo don kallon 'yan fim da mawaka wadanda muke kallon su a can (Nijar) lokacin muna yara.
To har Allah Ya sa na shiga sutudiyon Ali Baba har aka min tayin waka, na ce ba waka na zo yi ba ganinsu na zo yi.
To kuma dai har Ali Baba Yakasai ya ban shawarar cewa idan ina son yin waka zan iya yi. A haka sai na gwada. Daga nan sai suka gane ashe ina da murya kuma zan iya yin waka.
To a haka dai asalin wakata ta fara.
Short presentational grey line
Aliyu Tanko: Za ki iya gaya mana yawan wakokin da kika yi?
Fati Nijar: Gaskiya ba zan iya fada ba amma dai ina nan ina tattara kundin wakokina da na yi da na fim da na siyasa da na aure da na alboms da nake yi.
In Allah Ya yarda idan na gama tattara kansu anan ne zan fadi yawan wakokina da na yi.
Aliyu Tanko: An kwana biyu ba a ji duriyarki ba, me ya faru?
Fati Nijar:Gaskiya da yake na dade ban yi albom ba shi yasa aka ji ni shiru, amma in shaa Allahu kwanan nan zan yi albom.
Fati Nijar
Aliyu Tanko: Kamar zuwa yaushe kenan?
Fati Nijar:Eh da yake na fara, dama wakoki shida ne kuma na yi hudu saura biyu in Allah Ya so zan kammala.
Aliyu Tanko: Kenan masu bin ki su shirya za su ji sabuwar wakarki ko kuma wakokinki sabbi da za su yi tashe nan gaba kenan?
Fati Nijar:Gaskiya ne (dariya). Don wakokina na wannan karon ba a taba yin irin su ba, kusan in ce kirkira ce ta musamman na yi a kan wakokin.
Short presentational grey line
Aliyu Tanko: Wato za a cashe kenan?
Fati Nijar:(Dariya) eh gaskiya kuma za a nishadantu sosai.
Aliyu Tanko: To batun zamantakewa fa yaya kike ciki, kin yi aure ne?
Fati Nijar:(Dariya) gaskiya ban yi aure ba amma ina niyya in shaa Allah.
Aliyu Tanko:Akwai saurayi a kasa kenan?
Fati Nijar: Akwai masoya dai da yawa.
Aliyu Tanko: Ba a riga an tsayar da daya ba kenan?
Fati Nijar: Ba a tsayar ba amma in Allah Ya yarda za a tsayar.
Aliyu Tanko: Ko an tsaya ana irin kwalisa ce irin ta mata?
Fati Nijar: (Dariya) A'a ba ruwan ido na tsaya ba, ina dai rokon Allah ne Ya zaba min mafi alkhairi. Amma in da kwalisa ce ai da....... (dariya).
Aliyu Tanko: To Allah Ya kawo nagari.
Fati Nijar: Ameen, ameen.




©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top