Wani likita da ya kware a kula da matsalolin mata, Habib Sadauki ya gargadi mata da su daina maimaita zanin da suka yi amfani da shi wajen kare jinin haila.
Sadauki ya gargadi mata game da yin haka cewa mafi yawan mata na maimaita amfani da irin wannan zani duk lokacin da suke haila saboda tsadar audugar mata.
Ya ce mata na iya kamuwa da cuta har da dajin dake kama farjin mace.
Ya yi kara mata da su tsaftace jikinsu a kowani lokaci ba sai lokacin da ake haila ba cewa yin haka zai taimaka wajen kare mace daga kamuwa da cututtuka.
Sadauki ya kuma yi kira ga gwamnati da ta rage yawan harajin da take karba wajen kamfanonin sarrafa audugan mata cewa yin haka zai rage farashin audugan.
KARANTA: Matsalar rashi da tsadar audugar mata ya sa mata ba su iya zuwa makaranta idan al’adar su ta zagayo a Najeriya
Idan ba a manta ba a wantan Janairu ne wasu matasa maza da mata tare da hadin guiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira ga gwamnati da ta rage farashin audugan da mata.
A bisa sakamakon bincike da ake yi ya nuna cewa ‘yan mata musamman ‘yan shekaru 15 zuwa 19 basu iya zuwa makaranta a duk lokacin da suke jinin al’ada a dalilin rashin kudin siyan audugan da za su saka.
Binciken ya nuna cewa akalla mace daya cikin mata 10 bata iya zuwa makaranta na tsawon kwanaki hudu zuwa biyar duk wata. Wanna ba ga ‘yan mata ya tsaya ba har da matan aure.
Bincike ya nuna cewa mata biliyan 1.2 a duniya na fama da wannan matsalar dake da nasaba da tsananin talauci.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment