Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
Shugabar Gidauniyar tallafa wa mabukata da marassa lafiya, wato Today's life Foundation Mansurah Isah ta bayyana irin matsalolin da take cin karo da su a fafutukar da take yi na tallafa wa mabukata da marassa lafiya in da har ta kai wani lokacin ma ta kan yi tunanin ko dai ta dakatar da wannan fafutukar da take yi Iya kacin abin da ta yi kawai Allah zai dubi zuciyar ta ya ba ta ladan abin da ta yi.
Mansurah Isah ta bayyana hakan ne ga wakilin mu Mukhtar Yakubu, a lokacin da suke tattaunawa dangane da irin nasarorin da Gidauniyar ta samu tun daga lokacin da aka kafa ta, in da ta fara da cewa "To gaskiya an samu nasara sosai, domin kuwa a tsawon lokacin da na samar da wannan Gidauniyar zuwa yanzu akwai mutane da dama da suka amfana ta dalilin ta.
Duk da dai tun kafin na samar da wannan Gidauniyar na dade ina tallafa wa jama'a amma da na kafa wannan Gidauniyar abin ya fi tsari Kuma mabukata sun fi cin gajiyar abin fiye da lokacin da nake yi a baya, don haka a yanzu zan iya cewa mun samar wa da mutane da yawa Musa Mata hanyoyin dogaro da kai ta hayar koya musu sana'o'i da ba su jari, kuma muna da bangare na samar wa mabukata abinci wanda aka safa ko kuma tsaba, wannan kokarin mun yi shi a cikin burni da kauyuka duk muna shiga domin kai Wa mabukata kayan tallafa.
Baya GA haka muna shiga asibitoci domin kaiwa marassa lafiya magani da kudin da Za su dan riki a hannun su, kamar bangaren mata masu haihuwa da kananan yara.
To irin haka dai mun samu nasarori sosai kuma har yanzu a kan haka muke, don haka ne ma kullum akan ji gida ko a kan hanya a tare ni domin gabatar mini da bukatar mara lafiya abin da na ji zan iya sai na yi, wanda kuma na ji ba zan iya ba Sai na nemi gudummawar mutane da suke son tallafawa.
"Tun da an samu nasarori, ko wanne irin matsaloli kike fuskanta a cikin gudanar da wannan aikin?
Sai ta ce" Har ga Allah babu abin da ya fi zame mini matsala kuma yake jefa ni cikin tashin hankali, kamar a samu mutum cikin yanayi na bukatar a ceto rayuwar sa, amma sai ka ga, wani ana cikin hada kudin da za a yi masa magani, sai Allah ya karbi ran sa, wannan abin yana tayar mini da hankali.
Wani kuma sai ka samu an hada kudin an je an dauki tsawon lokaci ana ta magani karshe sai Allah ya karbi ransa. Wata kuma matsalar da ta fi tayar mini da hankali ita ce, mutum ya zo da rashin lafiyar sa an nemi kudi don a yi masa magani, sai ya ce shi ba haka yake so ba.
Misalin da zan ba ka shi ne akwai wata yarinya da take fama da ciwon daji a hannun ta muka yi ta fafutukar hada kudin da za a yi aikin kuma daga karshe dai an samu, muka je asibiti za a yi aikin, Sai likitan ya ce sai dai a yanke mata hannun in dai ana so ta samu lafiya, amma, abu mafi tashin hankali, sai iyayen ta suka ce ba su yarda a yanke mata hannu ba. To ba yadda muka iya, sai muka hamura, tun da yar su ce.
To irin wannan tashin hankali Sai wani lokacin na rinka tunanin ko dai na hakura da wannan abin, amma dai har yanzu ina nan ina ci gaba"
Daga karshe ta yi kira ga masu wadata da su rinka shiga asibiti ko wasu wurare da ake bukatar bayar da taimako su ga yadda al'umar Annabi suke cikin wani yanayi na bukatar taimakawa.
©HausaLoaded
Post a Comment