https://ift.tt/2Z3pfZw
Ya zama dole mace ta yarda mijin ta shi ne shugaba a kan ta, ko da kuwa ta girme shi da shekaru, ko ta fi shi kudi, ko ilimi, ko matsayi, ko karfi kodai wani abu na rayuwa. Ki tuna fa shi ne ya je har gidan ku ya nuna sha’awar kasancewa tare da ke na tsawo wani lokaci da bashi da karshe sai fa in mutuwa ta zo. Shi ne yake da hakkin kula da ke dangane da ci, sha, tufafi, matsugunni (wato gidan da kuke zaune) da kuma biya miki bukatar da babu wanda ya isa ya biya miki banda shi (wato . Allah ya fada a cikin littafin sa “maza sune Hanyoyin girmama mai gida suna da yawa. Sun hada da:
Boye sunan mai gida: wasu matan kawai sai ka ji suna kiran mai gida da sunan sa kai tsaye. Gaskiya yar uwa in kina so ki samu karin matsayi a wurin mai gidan ki dole ne ki boye sunan sa. Zaki iya cewa mai gida, baban wane/wance, doctor in likita ne, engineer in engineer ne, honourable, darling, sweetheart, sweety, bestie, nawan, the one, my heart, my love, k’ok’on zuciya ta da sauran su.
Yin kasa da sauti in kina magana da shi: mace ta gari itace wacce bata daga muryar ta idon tana magana da mijin ta, ko da kuwa ran ta ya baci. Yin hakan zai iya fusata shi kuma ta yiwu ma har yayi abin da bai kamata ba. Idon kika fahimci cewa ya hau sama, ran sa ya baci, sai ke kuma ki sauko, kuma ki yi masa magana mai dadi.
Bashi hakuri in kin yi laifi: dole ne mace in tayi laifi ta bada hakuri. Wasu matan in sun yi laifin ma aka fada musu sai su fara musu, suna kokarin kare kan su. Mace ta gari ita ce wacce in tayi laifi zata yarda tayi kuma ta bada hakuri tare da cewa inshaallahu ba zata sake yin irin haka ba. Yar uwa ta, abin da ya fi miki kyau ma shi ne ke ya kamata ki fara sanar da mijin naki laifin ki, sannan ki bada hakuri. Wasu mazajen in suka ga abu na laifi da fada zasu fara. Amma in ke kika fara sanar da shi sannan kika bashi hakuri, to inshaallahu komai zai zo da sauki
Daukar shawarar sa: idon mijin ki ya baki
shawara akan wani abu ya kamata ki girmama ra’ayin sa in har bai ci karo da addinin Musulunci ba. Wannan shi zai tabbatar masa da cewa kina girmama shi.
Wannan yana da matukar muhimmanci. Wasu matan kafar su kamar tana musu kaikayi, miji yana fita zasu dauki gyale, sai gidan makwafta ko gidan kawaye. Gaskiya hakan ba hali ne na gari ba. Allah madaukakin sarki yace “Kuma ku lizimci gidajen ku......”. Kin ga kenan a addinince ma dole ne ki zauna a cikin gidan ki, domin shine zai kare miki mutuncin ki a matsayin ki na mace, mai daraja. Ga wasu shawarwari dangane da wannan:
Yar uwa ta ki tuna fa dakin mijin ki shine rufin asirin ki. Ki tuna mata nawa ne basu samu damar yin aure ba? Wasu kawayen ki ne, wasu yan unguwar ku da sauran su.
Ki sani dole ne in zaki fita, ki fita da izinin mijin ki, kuma wajibi ke ki tsaya a iya inda kika ce zaki je. Wasu matan zasu tambayi izinin zuwa gida daya ko biyu amma zasu iya shiga gidaje goma. ‘Yan uwa na ku ji tsoron Allah.
Idon kina fita aiki, ya kamata ki kiyaye kan ki daga abokan aikin ki, ki rike amanar mijin ki a wurin da baya nan. Wasu mazajen sun amince wa matan su amma su matan zasu iya cin amanar su. Ki sani fa, wasu mazan zasu rinka kula ki ko da kuwa sun san kin yi aure kuma sun san mijin naki, musamman ma in kina da kyau kuma ke fara ce, kin san mafi yawan maza suna son farar mace har ma zaki ji wasu suna cewa “fara ko ‘yar gidan sarkin mayu ce”. ‘Yar uwa ta dole ki lura da irin wadannan domin komai kamun kan ki sun san yadda zasu shawo kan ki, dole ki kula su. Misali akan wannan shi ne, wata matar aure tana aiki a wata ma’aikata, sai ya kasance akwai wani mutum da yake son kula ta, amma bata so. Sai ya fahimci hakan, amma saboda tsananin naci bai rabu da ita ba. Sai ya samo wata dabara, ya fara yabon ta, duk abin da tayi na kirki sai ya fada. Daga karshe sai ya kasance ko sabon kunshi tayi ko kuma dai wani abu sabo in har bai gani ba bata jin dadi. Kun ga kenan tun bata so har ya kasance yanzu ita take neman ya kula ta! Kuma fa ku tuna tana da miji, kuma ba shine mijin ba. Daga karshe sai Allah ya taimake ta aka yi mata transfer daga wajen aikin nata zuwa wani waje na daban. A haka ne ta samu ta rabu da shi.
Haka zalika, ga matan da suke fita aiki, ku ji tsoron Allah in kun fita daga gida kar ku tsaya ko ina sai wajen aikin ku, haka kuma in kun dawo kar ku tsaya a ko ina sai gidan ku. Wasu matan suna amfani da aikin su sai su shiga kasuwanni ko malls ko super market su yi ta yawo da sunan sayayya suka je. Gaskiya hakan bashi da kyau. Ki tuna fa, yaran ki in sun dawo daga makaranta suna bukatar ganin ki, haka kuma mijin ki ma in da wuri yake dawowa daga wajen aikin sa yana bukatar ganin ki.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment