Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Babu wani lokaci da 'yan fim suka shiga siyasa da karfin su kamar zaben 2019 da ya gabata, don kuwa kusan babu wani dan fim da bai shiga harkar siyasa ba, Sai dai wasu kadan daga cikin su.

Rukayya Dawayya tana daya daga cikin Mata' 'yan gaba gaba a cikin 'yan fim da suka taka muhimmiyar rawa a cikin siyasar, kuma a yanzu an gama harkar siyasa don haka ne Wakilin mu Mukhtar Yakubu, Yayi Tattaki don jin ta bakin ta dangane da rawar da suka taka a fagen siyasa, har ya Tambaye ta ko kwalliya ta biya kudin sabulu? Kuma Wana darasi 'yan fim suka Samu?

Da farko dai ta fara ne da cewa "Harkar siyasa dai mun yi ta kuma mun Samu darasi, kodayake ni daman ina yi amma na fi bada karfi a wannan zaben da ya gabata, don a wannan zaben na yi siyasa ta Kano, na yi ta Katsina, in da nan ne asali na kuma na yi ta Jigawa, sannan na yi ta kasa gaba daya domin da ni aka yi yawon yakin neman zaben Shugaba Buhari a kasar nan babu inda ban zagaya ba, don haka zan iya cewa duk wata gwagwarmaya da ni aka yi.

Ta Kara da cewa "A yawon da muka yi na gane cewar, mu ne ma ya kamata mu yi siyasa don mu ne muke da farin jinin mutane don haka Wanda ya ke fitacce kuma jama'a suka San shi to shi ne ya kamata ya fito ya tsaya takara, don haka ni wannan ma ya Kara mini karfin gwiwar a zabe na gaba zan fito na tsaya takara, kuma ina da karfin gwiwar zan Samu nasara".

Ta ci gaba da cewa"Mu da muke harkar fim kowa ya San muna harka ne ta mutunci ba a same mu da wani abin fada ba, don haka muna da kima da mutunci a wajen mutane, kuma irin mu suke nema, don haka ma 'yan siyasa suke hada Kai da mu domin su Samu nasara.

Da muka tambaye ta dangane da irin kallon da wasu mutane suke yi wa 'yan fim na Rashin Kamala, da Muggan Dabi'u Sai ta ce;

Ai ka ce wasu, ka ga ba duka ba ne, mafi yawan mutane suna yi mana kallon mutunci, shi ya sa ma aka sa mu a gaba domin neman jama'a a wajen zabe, don haka masu wannan tunanin ma, yakamata su canza".

Daga karshe ta yi Kira ga 'yan fim da su ci gaba da kare mutuncin su a duk inda suka samu kansu.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top