Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Fitacciyar jaruma Masa'uda' Yar Agadas wadda aka fi sani da Zuby a cikin shirin Dadin Kowa ta bayyana harkar fim a matsayin harkar da duk Wanda ya samu daukaka to sai masu hassada da bakin ciki su rinka jin haushin ka saboda daukakar da K samu.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu Mukhtar Yakubu, dangane da yadda ta samu kanta a cikin masana'antar, da kuma yadda a yanzu ba a ganin ta a cikin shirin Dadin Kowa tun daga zangon farko, in da ta fara da cewar "To daman ni ina yin harkar fim ne, sai kuma na samu kaina a cikin shirin Dadin Kowa, don haka ni daman ina yin fim kuma na sa kudi na da dama na yi finafinai nawa na kaina, kuma da harkar shirin Dadin Kowa ta zo sai aka yi da ni.

Sai dai abin da na fi jin dadi shi ne, shirin Dadin Kowa shi ne ya daukaka ni a duniya Kowa ya sanni, duk inda na shiga za ka ji ana cewa Zuby, don haka, a nan na fi samun daukaka.

Ta ci gaba da cewa" kuma dalilin da ya sa ba a gani na, a Dadin Kowa, to ka san shiri ne mai dogon zango, don haka ana tafiya ne ana daukar wasu ana zubar da wasu, amma dai ba abin mamaki ba ne, idan nan gaba an sake dawowa da ni.

Amma dai na godewa Allah, lokacin da na fara fim babu Wanda ya sanni, tun da na fara shirin Dadin Kowa duk duniya an sanni, babu inda zan zaga ba a kira suna na ba. Yadda jarumin da ya yi fice zai shiga waje a kira sunan sa, ni ma haka ake kiran suna na.

Abubuwan da ban taba tunanin zan same su ba, a harkar Dadin Kowa na same su, in da ban taba tunanin zan je ba, to na je ta dalilin. Dadin Kowa.

Ko wanne irin matsaloli kika samu a rayuwar ki ta harkar fim?

Sai ta ce "To gaskiya na hadu da matsaloli sosai da kuma kalubale, da dama, irin ka ga wani ka samu wani abu ya na hassada yana jin haushi,sai ka ga wani yana son ka a fili sai ka tafi kuma ya zage ka, to na fuskanci irin wannan matsalar da dama, amma ni dai ina ina yi musu fatan alheri.

Daga kashe ta yi kira ga abokan sana'ar ta da su daina kyashi da hassada domin kuwa ba abu ba ne mai kyau.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top