Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa ta kannywood, Maimuna Muhammad, ta bayyana mafi yawan mazajen da suke zuwa wajen su da sunan suna son su a matsayin mayaudara da suke fakewa da soyayya domin biyan bukatar su.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu Mukhtar Yakubu, a game da irin kallon da ake yi wa 'yan fim na mayar da hankalin su kan rayuwar duniya fiye da lamarin aure, duk kuwa da dumbun masoyan da ake ganin suna da su, in da ta kada baki ta ce;

"To ka San kowa da irin matsalar sa, kuma na fuskanci abin da Maza suke yi a harkar fim ya fi na Matan, amma na matan shi ya fi fitowa fili, don yanzu idan har mace ba ta yi taka tsan tsan ba da namiji sai ya kaita ya baro.

Domin bari na fada maka, Mafi yawan Zantukan da Maza ke zuwa suyi mana na cewar suna Son mu ba komai ba ne Illa dadin Baki da Karya tsagwaranta.

Sai mace ta tara samari, ko sun Kai dari, da wuya ta fitar da guda biyu da suke son ta tskani da Allah, sauran duk na banza ne, In za ki yi harka ku yi su ba ki kudi su yi tafiyar su.

Wannan ba sai matan da suke harkar fim ba suke samun matsalar kowacce mace idan ka zauna da ita Sai ta kawo maka Wannan matsalar daga maza, don haka duk masu fadar cewar mun ki yin aure ko mun dade ba mu yi ba to ga irin matsalar da muke samun kan mu a ciki.

Musamman ma 'yan fim don haka muna son auren wanda Za su so mu tsakani da Allah Amma mun rasa aure ko yaushe a shirye muke in har mun samu wanda ya ke son mu tsakani da Allah ba mayaudari ba.

Tun da dai Maimuna ta gano Wannan matsalar wane Kira za ta yi ga matan da suke fuskantar Wannan matsalar?

"To ya kamata dai mu zauna mu yi wa kan mu fada tun da mun san halin mazan ga yadda suke, don haka mu rike mutuncin mu da darajar da Allah ya ba mu ta 'ya'ya mata ta haka ne kawai za mu nema wa kan mu 'yanci a wajen mazaje masu mummunar manufa a kan mu.'



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top