Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
Tsawon lokacin da aka shafe ba a ganin fitacciyar jaruma Zainab Indomie ya sanya mutane da dama suke tambayar ko a wanne hali jarumar take ciki a yanzu?
Babu shakka abu ne mai wahalar gaske a ce an manta da jaruma Zainab Indomie a cikin masana'antar finafinai ta kannywood, musamman idan aka duba irin tasirin da jarumar ta yi a shekaru goma da suka wuce.
Domin kuwa ta taka rawar da har yanzu babu wata Jaruma da ta kai kamar ta, wannan ya sa har yanzu masu kallon fim suke son su ganta a fim, don haka jarumar ta tafi da tasirin ta da har yanzu ake kallon ta da shi, Irin wannan yanayi ne ya sa har yanzu ba a manta da ita ba.
Daya daga cikin abin da ya sa Zainab Indomie take da tasiri shi ne, surutun mutane ba ya tayar mata da hankali, don haka ta yarda matsalar ta, matsalar ta ce, duk abin da za a yi ta fada a kan ta bai shafe ta ba, Hakan ta sa duk wani abu da take yi idan an cika duniya da labari a kan ta Sai ta nuna halin ko in kula ita ba ta ma San ana yi ba.
Tana da tasiri a wajen furodusoshi da Daraktoci don kuwa ba a taba samun jarumar da ta wahalar da su ba kamar Zainab Indomie, domin sun sha jiran ta Tsawon kwana biyu ko uku tana bacci suna son ta tashi ta yi musu aiki, amma wani lokacin daga ta tashi, Sai a nemeta a rasa, amma haka za a tafi yawn neman ta a lallabota don ta zo ta yi aikin.
Ta sha yin furucin kada wani furodusa ya kara saka ta a fim, amma dai sai a je a lallabota a yi kamun kafa da wanda take jin nauyin sa, ta zo tayi aikin.
Rayuwa kenan! Yau Ga shi ana harkar babu Zainab Indomie, ba kuma harkar ce ta daina yi da ita ba, ba kuma an daina yayinta ba, za a iya cewa ma ita ce ta daina yayin fim din, a yanzu idan kana neman ta babu wani tabbas na wajen da za ka same ta, sai dai kawai inda ka ci karo da ita, ita daman harka ta duniya ba sai ka mutu ba ake daina ji ko ganin ka ba, wannan kuma kalubale ne ga jaruman da suke haskawa a wannan lokacin ko Hakan zai zame musu darasi?
©HausaLoaded
Post a Comment