Kamfanonin sadarwan Najeriya sun yi ca akan kiran ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, cewa a rage kudin Data cikin kwanaki biyar masu zuwa saboda ya yi tsada da yawa.

Kamfanonin sun bayyana cewa hakan ya sabawa hankali kuma ba zai yiwu ba. Daily Trust ta bada rahoto.

Kungiyar kamfanonin sadarwan Najeriya ALTON ta bayyanawa manema labarai cewa umurnin da ministan ya bada zai kori masu sanya hannun jari daga kasar kuma hakan kama karya ne.

Shugaban kungiyar, Injiniya Gbenga Adebayo, ya bayyana hakan ne a wani hirar tarho da yayi da wakilin majiyarmu.

Yace: "Bai kamata a rika yiwa NCC kama karya ba saboda kada aka kashe nasarorin da aka samu bangaren sadarwa a shekarun baya."


"Ban san ta yaya gwamnati ke shirin aikwatar da hakan cikin kwanaki biyar ba. Shin sun yi tunanin yadda kasuwancin ke da tsada a kasar da muke ciki?"

"Ta wani dalilin za su rika kokarin yiwa NCC kama karya ta hanyar sanyasu yin abin da bai zai yiwu ba? Shin sun sani cewa ba kawai zama mukeyi mu sanya kudi ba?"

"Bamu san abinda ya sa aka bada umurnin ba amma maganar gaskiya shine bamu san yadda hakan zai yiwu ba."

A jiya, Gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC, ta tilasta ma kamfanonin sadarwar tare da samar da wani tsari da zai tabbatar da rage farashin sayen ‘Data’ da yan Najeriya suke yi, domin kuwa yan Najeriya na kokawa a kan tsadarsa.

Ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin gudanarwar hukumar NCC a karkashin jagorancin Sanata Olabiyi Durojaiye.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top