Legit na Wallafa labarin.
Wasu ma'aura 'yan asalin kasar Pakistan sun gano cewar su 'yan uwan juna ne bayan fiye da shekaru 24 da aurensu, kamar yadda kafar yada labarai ta SMACK ta rawaito.

Ma'uaratan, wadanda uba daya ne ya haife su, sun rabu da juna tun yarinta sakamakon mutuwar iyayensu, kuma suka fada hannun masu riko daban-daban, lamarin da yasa basu kara ganin juna ba, har sai bayan da suka shafe fiye da shekaru 24 suna zaune tare a matsayin mata da miji.

"Mun dauka cewar aurenmu tamkar kowanne irin aure ne, a tunaninmu, mu 'yan uwan juna ne kawai da suka hadu ta dangi," a cewar mijin, Abdul Rahim, mai shekaru 47.

"Ashe kowa a gari ya san cewa mu 'yan uwan juna ne, da uba daya ya haifa, amma babu wanda ya iya samun karfin gwuiwar sanar da mu gaskiya sai yanzu," a cewar matar, Aisha, wacce ta auri dan uwanta da suke uba daya.


Sai dai wata mai ilimin al'adun mutane, Juliane Edwards, wacce keda ilimi a kan yadda ake aure a tsakanin 'yan uwan juna a kasar Pakistan, ta ce bata yi mamakin faruwar hakan ba.



"Al'ada ce a wurinsu. Idan har aure a tsakanin 'yan uwa na kusa ko a cikin dangi bai zama laifi ba, aure a tsakanin 'yan uwan da uba daya ya haifa bai kamata ya zama abin mamaki ba," a cewarta.

Sanna ta kara bayyana cewa, "na gani yafi sau a kirga a kasar Pakistan inda mutumin da matarsa ta mutu zai zabi daya ko fiye da haka daga cikin 'ya'yansa mata, a daura musu aure, ya mayar da su matansa."

"Na taba jin labarin wani mutum da ya haifi wata mummunar yarinya da ta rasa miji, shi kuma ya tilasta dan cikinsa ya aureta a matsayin hukuncin kasancewarsa malalaci," a cewar Juliana

A shekarar da ta gabata ne wata kotun Sharia ta tarayya a kasar Pakistan ta shiga bakin duniya bayan ta ki raba auren wata mata da ta shigar da korafin cewa an daura mata aure da dan uwanta, kotun ta sanar da matar cewa, "kasancewarku 'yan uwan juna da uba daya ya haifa, bai isa dalilin da zai sa kotu ta amince da rabuwarku ba a tsarin Shari'a."

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top