Barkanmu da warhaka tare da fatan ana lafiya. Yaya shirin Sallah? Allah Ya nuna mana amin. Sallah dai kamar kowace shekara an fi sanin mata da dama da yin kunshi da kitso da dinkin kayan Sallah da kuma sauran shirye-shirye.

 A yau ina so in sake jawo hankalinku zuwa ga irin kwalliyar da ya kamata a yi da Sallah domin idan akwai wadda ba ta riga ta sayi lalle ba sai ta yi maza ta saya. Yana da kyau a hada wannan kwalliyar da dilke da kuma kurkum domin samun ingantacciyar kwalliya.

• Yana da kyau idan an zo kwaba lalle sai a kwaba shi da ruwan lemun tsami da sukari domin ya kama da wuri. Za a iya yin kwalliyar lalle da zanen fulawa a tafin hannu ko kuma a tafin kafa.

• Kurkum; kurkum na taimaka wa mace yin haske amma an fi yawan amfani da shi ga amare a lokacin aurensu. Amma kwalliya a yanzu ba sai ranar auren mace ba, musamman ga masu aure za su iya biya a yi musu kurkum a jikinsu domin samun fata mai sulbi da santsi da kuma haske.

• Dilke; ana yin dilke ne kafin a yi kurkum. Domin dilke na cire duk dattin da ke cikin fata tas yadda fata za ta yi sumul da kuma sanya ta sheki.

• Kaya; Ana so a dinka kaya mai kyau sabo wanda za a je Idi da shi ga wadda take da hali. Akwai dinkuna masu kyau wadanda mace mai aure za ta iya sanyawa a cikin gida domin burge maigida. Idan ko za ta je masallaci sai ta sanya hijabi don kada ta jawo hankali.


• Kitso: Idan za a iya yin hakuri, kananan kitso sun fi kyau a kan fatar mace don haka yana da kyau a samu wadda ta iya kitso ta zana kanana kuma yadda za ta yi kyau.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top