Barkanmu da Sallah tare da fatan ana cikin koshin lafiya? Allah Ya karbi ibadunmu na alheri Ya kuma maimaita mana wannan rana. Ina so na janyo hankalin ’yan uwana mata musamman matan aure da su kasance masu yin ado ga mazajensu, kamar yadda aka yi mana nasiha a lokacin da muke amare. Don haka a dage wajen amfani da turaren wuta domin tsaftace muhallinmu da dakunanmu saboda jin dadin iyalanmu.
Ga kadan daga cikin hanyoyin da suka kamata uwargida ta bi don ganin an samu biyan bukata:

==> Uwargida ta tabbata ta dage wajen amfani da turaren wuta ; a samu kaskon turare a zuba garwashi sannan a zuba turaren wuta a dora kabbasa a kai sannan a dauki zanin gado a rufa a don turara shi a duk lokacin da zaa shinfida a kan gado hade da labule da kuma kayan da za ta sanya a jikinta. Lallai wannan turare na dadewa sosai a jiki.

==> Kitso; uwargida ta dage da yin kitso a kalla sau biyu a wata musamman idan ta kasance mai yawan ‘ya’ya. Amma an fi so a duk sati maigida ya rika ganin matarsa da sabon kitso. Ta kasance tana shafa wa gashinta mai don hana fesowar amosanin ka da kuma rage tsinkewar gashi.

==> Lalle; jan lalle irin namu na gargajiya na da kyau sosai. Uwargida ta kasance wajen shafa wannan lalle a tafin kafarta a kodayaushe domin ban da adon da yake yi yana kuma bayar da kariya ga lafiyar mace. Idan ba za ta samu damar yin lallen a kodayaushe ba, to ta kasance tana shafawa a kalla atafukan hannayenta.

==> Dinki; kada uwargida ta ce za ta daina yi wa maigida kwalliya saboda ta manyanta. Ta dage wajen yin dinki irin na zamani don burge maigida a gida amma dai kada ta manta da sanya hijabi a duk lokacin da za ta fita zuwa unguwa.

==> Gyaran fuska; a kwai wata irin kwalliya wacce ’yan matan yanzu ke yi. Kamar sanya jan baki da gyaran gira. Sannan ina kira ga mata da su dage wajen yin kwalliya irin ta zamani, ko da sun manyanta ne, don haka na karfafa soyayya a tsakanin ma’aurata.

==> Daurin dan kwali; idan Uwargida tana gida ta kasance mai yin daurin dan kwali irin na zamani don jan hankalin maigida. Kada ta bari a bar ta a baya ta rika ganin wai ta tsufa. Za ta iya koyon irin wannan daurin dan kwali daga wajen ’ya’yanta mata ko kuma ’yan uwanta da kuma makwabta. Yana da kyau kowace mace komai tsufanta ta rika tafiya da zamani.

A yi sallah lafiya.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top