Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai kira taron Shugabannin Yankin Tafkin Chadi domin yin wani taro kan matsalar tsaro.
Buhari ya ce za a yi wannan taron ne a cikin wannan zango na sa na biyu da aka shiga, a Abuja domin yin gangamin yi wa masu ta’addanci yunkurin murkushe shi kurmus.
Taron inji Buhari zai gudana ne a lokacin da aka zo bikin Ranar dimokradiyya, 12 Ga Yuni, a Abuja.
Buhari ya yi wannan sanarwa ce a lokacin da ya ke ganawa da Shugaban Kasar Chadi, Idris Deby, a Makkah, Saudi Arebiya, lokacin da suka je Taron Shugabannin Kasashen Kungiyar OIC.
Shugabannin biyu na Najeirya da Chadi sun yi taron a jiya Asabar.
Buhari ya ce tunda dai zabe ya rigaya ya wuce, to zai samu damar murkushe Boko Haram da ‘karfin tsiya.’
Ya ce taron da za su yi, zai samar da hanyar da za a bi a kakkabe Boko Haram kwata-kwata a yankin kasashen da ke kan iyaka da Tafkin Chadi.
Kasashen da suka yi iyaka da Tafkin Chadi sun hada da Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Kamaru da kuma Chadi.
Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce shugabannin biyu sun amince cewa lokaci ya yi da za su zauna su amince a kan yadda za a sauya salon yaki da ta’addancin da ya ki ci, ya ki cinyewa.