Da farko dai a ranar Juma’a Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga lamarin, biyo bayan kiran da aka yi kan ya sanya baki da kuma yawan kira daga dattawan arewa yayinda rikici tsakanin gwamnan da sarkin ke kara daga hakula a jihar.
Sanya bakin Shugaban kasa a lamarin na zuwa ne kwana daya kafin wa’adin da gwamnatin jihar ta dibar ma sarkin akan yayi bayani game da kudaden masarautar.
A taron sulhun da aka gudanar a daren ranar Juma’a a Abuja, gwamnan da sarkin sun amince sun janye takobinsu don ra’ayin Kao da kuma rage fargaba domin guje ma karya doka da oda.
Koda dai har yanzu babu cikakken bayani kan abunda ganawar ta kunsa, wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya jagoranci ganawar wacce ta samu halartan yan tsirarun manyan mutane.
®Legit.ng
©HausaLoaded
Post a Comment