Mene Laifun Kwankwaso Akan Gaskiyar Da Ya Fadawa Malaman Izala?

Waishin menen laifun kwankwaso akan gaskiyar da ya gayawa malaman izala na jahar kano daga babban editan jaridar Hausa Trust

jamaa barkanmu da wannan rana da fatan mun wayi gari lafiya magana ce akan maganar da madugun kwankwasiyya eng, Dr Rabi u Musa Kwankwaso ya gayawa malaman izala na jahar kano,

maganar da kwankwaso yayi yayita ne akan bun bayan gwamnati da wasu daga cikin malaman kano suka nuna karara

Abun mamaki anan shine wa yannan malamai ba a taba jinsu sun futo sun fadi laifun wannan gwamnati ba kowa yasan irin badakalar da ake zargin gwamna ganduje da ita akan wasu makudan daloli amma wa yannan malamai baa taba jinsu sun futo sun magana akan wannan al amari ba amma yanzu kuma sun futo suna kiran yan jam iyyar PDP da cewar barayine bayan kuma bahaka ya kamata malami ya zama ba saboda haka a raayina banga laifun kwankwaso ba akan wannan magana,

kuma wani abu guda daya dana lura dashi kwankwaso yayi ikirarin cewa lokacin da yake gwamna akwai malaman da yabawa mota akan suyi daawa amma suka sayar da motocinnan sannan akwai wa yanda suka muslintar da inyamurai anma suka koma suna neman wa yannan inya murai sannan da sauran batu tuwa dai da yayi amma haryanzu malamannan babu wanda yazo yace kwankwason karya yake, sai dai kawai kaji suna cewa yaci zarafun malamai yaci zarafun gemu,

kuma a fahimta ta kwankwaso ba mutuncin gemu yaci ba tunda cewa yayi wasu daga cikin wannan malamai zaka ga sunsa wata suama ta karya a fuskarsu kuma wannan suma da suka sa munsan ta karyace,
acikin wa yannan malamaine kwankwaso yake cewa an wayi gari an kamasu da manyan laifuka sune suka musuluntar da inya murai sannan suka koma suna neman su kwankwaso yace wa yannan mutane sunanan basu da iyaka

to shin dan Allah wa yannan mutane idan kwankwaso ya kirasu da masu sumar karya yayi laifi kuma haryanzu malamannan babu wanda ya futo ya karyata wannan al amari,

Post a Comment

 
Top