Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana gazawar gwamnatin maigidanta

- Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya don jan hankalinsa akan abubuwan da ke wakana a kasar

 - A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana wuraren da gwamnatin maigidanta ta gaza.

A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar. Don haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya a matsayin hanyar jan hankalin Shugaban kasar domin sanar dashi rashin jin dadinta akan abubuwan da ke wakana a kasar.

A wani jawabi daga hadiminsa, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yayi maganar ne lokacin da ya taka rawar mai masaukin baki na hukumar tantancewa na wata kafar sadarwa, wato Penpushing Media a dakin karatunsa na Abeokuta.

 Majiyarmu tat samu wannan daga jaridar legit.ng/hausa a  jinjina wa uwardidar Shugaban kasar, cewa matsayarta abune mai kyau ga ci gaban kasar.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top