Saboda haka kada a zaci za suyi halin mazan da!

Mu matan, MATAN DA NE?
A,a!
To meyasa muke son mu zama matan yanzu masu son namiji ba saboda Allah ba, sai saboda abin da zai masu?
Mun ki masu son gaske, sai su suyi mana?
Yaya zasu zama mana na kirki?

Tabbas akwai matan kirki masu godiya amma ba yawa.
Ban ce DUKA MATA ne masu rahin kirki ba...don bana cikin su. 

Amma ai ya kamata muyi la'akari da wannan juyin da ya same mu. 
JUYIN ZAMANI.
Mu sani ba da gangan maza suke yin abinda suke ba da sunan rowa.

Su a wurin su tsare mutuncin su da na abin da suke da shi ne, shiyasa basa son yin wa mata hidima.

Domin gani su ke ko sun dage sun nema, sun bayar, ba shi zai sa a ga kiman su ko kokarin su ba, balle a gode.

Ba su mazan su ka gaya man ba, a'a nazari na yasa na gane.

Amma canjawan nan, da maza da yawa suka yi lallai yana da ban ta kaici ga mata.

Amma kafin mata su cigaba da korafi a kan wannan sabon hali na ROWAN da maza suke yi, sai an san ZAMANI ke tasiri a yanayin da suka samu kan su a ciki...kuma wannan ya sa mata cikin mamaki.

Abin bakin ciki shi ne, maza sun riga sun chamfi mata da cewan wai wayo za'ayi masu...sun dage da cewan ana son raina masu hankali.
Maza masu aure kuyi kokari. Marasa auren kuyi hankuri.
To abin da ya kamata muyi shi ne muyi kokarin yin wa juna adalci.
Mu rinka zurfin tunani don Allah, kuma tare da yin wa juna uzuri.

ZAMANI ne.
Allah Kyauta.

Daga uwa idris


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top