Ta tabbata gobe Talata take Sallah yayin da sabon jaririn watan Shawwal ya bayyana a kasar Saudiya. Hakika gobe ne 1 ga watan Shawwal na shekarar Alif dubu daya da dari hudu da arba'in bayan hijirar fiyayyen Halitta daga birnin Makkah zuwa Madinah.

A gobe da ta kasance Talata, 4 ga watan Mayun 2019, za a gudanar da shagulgula na bikin karamar Sallah a kasar Saudiya yayin da jaririn watan Shawwal ya bayyana a Yammacin yau bayan an kai azumi na ashirin tara.

Ko shakka ba bu addinin musulunci ya shar'anta yin azumin farilla na tsawon kwanaki ashirin da tara ko kuma talatin a watan Ramadana inda kuma ake gudanar da bikin karamar Sallah watau Eid Ul Fitr yayin da watan jinjirin watan Shawwal ya bayyana.

A yayin da al'ummar Musulmi ke kirdado tare da laluben bayyanar sabon watan Shawwal a Najeriya, a yau ne za a kai azumi na 29 a wannan mafificin wata na Ramadana da aka fara gudanar wa tun a ranar 6 ga watan Mayun 2019.


Jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Muhammad Sa'ad, ya hori al'ummar musulmi a Najeriya da su zura idanu tare da fita wajen laluben jaririn Shawwal daga yau daren Talata.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top