Ba'a tilasta soyayya. 

Sai dai kawai ka yi kokarin jadada ta a wajen wanda kake so...tare da jira ka gani ko ta amince, ko ba ta amince ba. 

Yawancin maza basa jira su ga ko ana son su, ko ba'a son su.

Su dai idan suna so, to shikenan!

Wannan ba daidai bane...kuma shika shikan SON KAI NE kace dole ne sai an so ka, don ka isa...to saboda me?

Haka ake yi?

Ai mata ba haja bane, mutane ne
ba wai wasu halitta ne ba daban da kai ba. 
Su ma mata suna da 'yan'cin zaben wanda hankalin su ya kwanta da shi, ko ace wanda suke so.

Amma kawai maza sai kuce don ku zabi mace da ido, ko da zuciya, shikenan sai ta kasance taku? 
Idan hakkan bai yiwu ba, sai kuce soyayya bata yi maku adalci ba.

Su matan basu isa su ce basu so ba?
Mata fa, mutane ne masu ra'ayi da kuma son abin da suke so... da kin abin da basa so. 
Saboda da haka yakamata maza mussaman ku lura da hakkan, don rage wa kai bacin rai, idan baku samu yadda kuke so ba.

Ku kuma mata ku sani cewan so ba a aljihu yake ba...a'a a zuciya yake.
So na kudi ba SO bane...domin wadanda kuke son kudin na su sun sani, kuma a hakkan zasu tafiyar da ku.

Kada kuji tsoron namiji mara kudi, sai namiji mara zuciya. 

Mara kudi mai zuciya yafi, idan dai yana neman su.

Kada kuma mu manta cewan mara kudin yau, shi ne mai kudin gobe.

Daga uwa idris


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top