Akwai wani zance da mutane ke yi game da soyayya.

Wannan zancen bai wuce cewan, wai soyayya KARYA NE, ko kuma cewan wai YANA KAREWA.

Eh...tabbas soyayya karya ne...idan ba DA GASKE a keyin shi ba?
Kuma yana karewa idan mutun YAYI da zai kare.

To don Allah Menene abin rashin ganewa anan?

Dalilain rashin ganewa biyu ne.
Na farko KAFIYA watau taurin kai, da dagewan cewan mutun ba zai yarda da maganan ilimi ba,sai dai nashi mummunar fahimta.
Na biyu, rashin sani.

Kamar yadda na ke fadi...soyayya GASKIYA NE!

Masoyan karya, su ke sa soyayyan GASKIYA ya zama KARYA.

A wannan zamanin matan da mazan, duk su kan yi karyan soyayya.
Sai wannan yaga laifin wannan, wannan yaga laifin wancan...don tsabar RASHIN GASKIYA!

Kuma duk masu karyar, akwai dalilan da yasa suke karyan.
Don SON RAI ne kawai da RASHIN TAUSAYI.
A sanina ba wanda baya son a so shi.

Saboda haka dan adam ya gada.

Kuma ko mun so ko mun ki, soyayya yana da tasiri.

Bance SHA'AWA ba fa!

Tabbas soyayya da sha'awan abokan juna ne...tafiyar su daya amma kowanne da MATSAYIN shi.

To yanzu a wannan zamani me ya kamata muyi a kan soyayya?

Ya kamata farko mu so don Allah.

Wanda ya ke wa mutane wuya...saboda basu da HALIN KIRKI ga karancin tsoron Allah...sai SON KAI na hauka.

Idan ba mu iya wannan irin soyayyar ba, to mu ma ba za'a so mu don Allahn Ba, mu ma.
A tuna duk abin da mutun ya SHUKA shi zai GIRBE!
Mun sani, mun ki sani...to laifin wa kenan?

Ance maza suna yaudara...ba dole suyi yaudara ba...tunda mata ma mayaudara ne?
Ance mata suna son kudi fiye da soyayya...to ba dole ba tunda mazan yaudara suka sani, kuma mata basa son yin biyu babu?

Kowannen mu na da laifi.

Ga satan amsa a wajen neman so.

IDAN KANA SO A SO KA, KA ZAMA ABIN SO MANA...tabbas zaa so ka. Shikenan!

Ba kawai daukan wanka shi ne neman so ba, aa hali shi ke sa so. Komin wanka ka, ko wankan ki idan babu tausayi da imani ba zaa iya so da ku ba.
Shiyasa mutane ke cewa so yana kare wa da zarar anyi aure ko haifuwa. 
Ba karewa yake ba, HALI ne ya kan fito a gane ko wanene mutun sai a wani lokaci zaman ya canja...soyayyar ta mutu!
Amma kuma, wa ya kashe ta, ita soyayar? 
KAI ko KE!

Mu rage kwadayi da keta da son kai sai mu dace, Abin Na Allah ne.

Yaudaran kai ga wanin mu ba kyau...
Mu daina mana?
An rinka hakkan kenan har illa MashaAllah?
Ba za'a chanja ba?
A samu kyakkyawan fahimta tsakanin juna mana?
Shine kawai!
A koyi tattauna wa da juna.
Lokacin boye boye da kame kame ya wuce fa.

Yakamata, i'war haka, mu daina RAINA WA JUNA HANKALI.

Kowa Ya fara chanji daga kan shi...ya tuba wa Allah.
Ko maza suna jiran mata su daina ne, su kuma mata suna jiran maza su daina nasu ne?πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
Wanne ne?

Allah Gyara! Matsala soyayya

Daga uwa idirs


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top