Legit.ng ta ruwaito Sir Jalal ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labaru daya kira a garin Kaduna a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni, inda yace El-Rufai ya fara takalar jagoran APC, Ahmed Bola Tinubu ne domin yana neman tsayawa takarar shugaban kasa.
El-Rufai da Sir Jalal |
“Baya ga burinsa na zama dan takarar shugaban kasa a 2023 a jam’iyyar APC, ko kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Farfesa Yemi Osinbajo, wanda shine dalilin da yasa yake neman rigimar Tinubu, El-Rufai na shirin kafa sabuwar jam’iyya don tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.” Inji shi.
Haka zalika matashin dan siyasan wanda ya tsaya takarar gwamnan jahar Kaduna a inuwar jam’iyyar APC a zaben 2019 ya bayyana ikirarin da El-Rufai keyi na yi ma wasu yan siyasa ritaya a Kaduna a matsayin shashanci, inda yace ba kansa aka fara zarcewa akan mulki ba.
Sir Jalal ya bayyana tsohon gwamnan jahar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi a matsayin wanda ya fara zarcewa a kujerar gwamna daga shekarar 1999 – 2007, sai Patrick Ibrahim Yakowa daya lashe zaben 2011 bayan darewa mukamin gwamna a shekarar 2010.
Daga karshe matashin dan gwagwarmayan ya zargi El-Rufai da yin bake bake a harkar mulki, baya son jin shawarar kowa, baya son ra’ayin kowa idan ba nasa bane, kuma baya kaunar yaga wani na gogayya dashi, inda yace wannan hali ne na shuwagabannin makarantun kauye.
®Legit.ng
©HausaLoaded
Post a Comment