Jaridar Daily Trust ta samu labarin abinda ya wakana cikin ganawar sulhun gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu da hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote da shugaban gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, sunka shirya.

Fadar shugaban kasa, musamman bangarar tsaro ta nuna damuwarta kan rashin zaman lafiyan da wannan rikici ka iya zama sakamakon dambarwan tsakanin sarki da gwamnan tun lokacin da aka kafa sabbin masarautu hudu da kuma binciken masarauta da badakala.

Wannan tsoro ya sabbaba hana hawan Nasarawa da Daushe a wannan shekara bayan an hallaka wani matashi a ranar hawan Sallah.


A makon da ya gabata, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da NSA Babagana Munguno, sun shirya wata ganawa a fadar shugaban kasa.

Majiya ta bayyana cewa kawo yanzu, an fasa tsige sarkin Kano inda gwamnan ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin haka.

Majiyar Daily Trust ta kara da cewa sun amince da cewa za'a fifita zaman lafiyan jihar Kano a sulhun.

Amma har ila yau, gwamnan da Sarki basu cimma matsaya ba inda kowanne yaki hakuri da bukatar dayan. Gwamna Ganduje ya lashi takobin cewa kafa sabbin masarautun Rano, Bichi, Karaye da Gaya na nan daram-dam.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top