- Ta ce za ta cigaba da binciken shi har sai lokacin da ta samo gaskiyar abinda aka yi da kudin
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana furucin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, inda yake cewa ba shine akawun masarautar Kano ba a matsayin maganar da bata kamata ba.
Hakan ya biyo bayan rahoton da hukumar ta bayar akan binciken da take yi game da cinye sama da naira biliyan uku da rabi, wanda masarautar Kano ta yi.
Rahoton wanda shugaban hukumar ya, Mr Muhuyi Magaji ya sanyawa hannu, sannan kuma aka bai wa manema labarai takarda guda daya ta rahoton a jihar Kano.
Sarkin Kano ya mayarwa da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje martani akan zargin da yake yi masa na cewar ya handame sama da naira biliyan 3.4, Sarkin ya bayyana cewa shi ya tarar da naira biliyan 1.8 ne kawai a asusun masarautar a lokacin da aka bashi sarauta.
Amma a wani sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa babu alamun gaskiya a maganganun da Sarkin yayi.
A binciken da hukumar ta yi anyi amfani da asusun masarautar na First Bank mai lamba 2005888452 sau 783, inda ake sanya kudi da kuma cirewa da sauran abubuwa da suka shafi banki, daga ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2o13, zuwa 6 ga watan Yuni, 2014, a lokacin marigayi Sarki Ado Bayero.
KU KARANTA: Murtala: Ya sanar da kotu cewa wallahi ba zai saki matarsa ba har sai ta biyashi sadakin naira miliyan 3.5 din shi
"Daga ranar 2 ga watan Janairu zuwa 13 ga watan Afrilu 2017, kudin da ya rage a asusun naira 432,338,412.98. Sannan an sanya kudi naira 6,784,146,335.73, sannan an cire naira 7,209,035,163.09," in ji shugaban hukumar.
Haka kuma kudin da ya rage a cikin asusun daga watan Afrilun 2017 naira 7,449,585.62.
"A takaice dai iya kudin da aka cire daga asusun a lokacin marigayi Ado Bayero naira 2,414,577,977.35.
"Shaidu sun nuna cewa Sarki Sanusi yana da hannu a cikin kashe naira 4,794,457,185.74 daga cikin kudin asusun masarautar na First Bank," in ji shugaban.
Haka kuma ana zargin cewa duk wani cire kudi da za ayi daga cikin asusun masarautar da umarnin Sarki Sanusi ake cirewa.
"Saboda haka duk wata magana da sarkin zai yi akan cewa ba shine akawun masarauta ba soki burutsu ne.
"Za mu cigaba da gabatar da bincike akan naira 3,432,090,797.94 da har yanzu ba a san wani muhimmin abu da aka yi da su ba," in ji shugaban hukumar.
®Legit.ng
©HausaLoaded
Post a Comment