Tsohon sakataren gwamnatin kasa ya nemi gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da ta tabbatar ba ta sabawa ka'ida ta shari'a ba a yayin takaddamar Masaurautar Kano da wargi ba ya kusantar ta.
Yayale wanda ya kasance tsohon shugaban ma'aikata gwamnatin Tarayya kuma tsohon Ministan Tsaro, ya ce duk da goyon bayan jam'iyyar adawa ta PDP, gwamnatin jihar Kano ta tuna cewa Sarki Sanusi ya kasance uba ga dukkanin al'ummar jihar.
Yayin ganawar sa da manema labarai ta hanyar wayar tarho, tsohon Ministan ya kuma tunatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje cewa ya kasance jagora ga dukkanin al'ummar jihar Kano duk da sabani na ra'ayin siyasa.
Yawale wanda shi ne mai rike da rawanin Ajiyan Katagum, ya gargadi gwamnatin Kano kan cewa muddin ta ci gaba gudanar da al'amura tare da mu'amalantar masarautar Kano kamar yadda ta ke yi a yanzu, babu shakka ba za a kwashe lafiya ba cikin ilahirin Arewacin Najeriya baki daya.
Ana iya tuna cewa gwamnatin Kano na zargin fadar Mai Martaba Sarki Sanusi da almundahar kimanin Naira biliyan 3.4 na masaurautar Kano. Sai dai yayin mayar da martani fadar ta ce abin da ta riska yayin cin gajiyar mulki bai wuce Naira biliyan 1.8 ba.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kafa kwamitin wasu gwamnoni hudu na jihohin Ekiti, Kebbi, Jigawa da kuma na Neja akan shiga tsakani tare da tabbatar da sulhu tsakanin gwamna Ganduje da kuma Sarki Sanusi.
©HausaLoaded
Post a Comment