Gidan hoton ya kasance na zamani, wanda zai bai wa ’yan birni da fitattun mata da sauran matasa har da ma manyan mutane damar daukar hotuna tamkar a kasashen waje.
Bude gidan hoton dai da Danja ya yi a na kallon sa a matsayin wata dabara ta raba kafa tare da fadada hanyoyin shigowar kudi a Kannywood, wato masana’antar shirin finafinan Hausa, domin hoto da bidiyo tamkar Danjuma da Danjummai ne.
An dai saba ganin yadda jarumai ke kashe kudi wajen dauko hayar masu daukar hotuna, domin fito da kyawunsu. Wasu na ganin cewa, bude gidan hoton da Sani Danja ya yi zai bayar da dama ga masu wannan sha’awa ta daukar hoto su samu a kusa kuma tare da wadanda su ka san abin da yadda su ke.
Binciken LEADERSHIP A YAU ya nuna cewa, gidan hoton ya na kuma da wani tsari na tafi-da-gidanka, inda za ka iya daukar hayar kwararrun masu daukar hoto, domin biki ko suna da taruka da dai makamantansu.
Bayanai sun nuna cewa, jaruman Kannywood da dama su na ta fito wa da kansu hanyoyin samun kudin shiga daban-daban, inda wasu ke bude shagunan sayar da kayan sawa na suturun zamani, kayan kwalliya da sauransu
©HausaLoaded
Post a Comment