Alamomi 7 Da Za Ka Gane Ka Kamu Da Ciwon Zuciya

 By Abubakar Abba :

Bugun zuciya har yanzu shine na daya da yan Najeriya suke fama dashi, inda hakan ya nuna cewar, a duk cikin mutane goma, uku na fama da ciwon. 

Alamomin sun hada da, jin zafi a qirji da yawan yin zifa da jin kasala har ila yau kuma akwai wasu sauran alamau. 

In har kana jin wadannnan alamun, ya kamata ka gaggauta ganin likita kuma ida ka ankarae da ciwon tunda wuri zaka samu sukunin magance da wuri.

 1. Kasala: Jin kasala tana daya daga cikin alamomin bugun zuciya musamman ga mata. Mutanen da zasu fara kamuwa da bugun zuciya zasu fara jin kasala kuma zasu ji sun kasa yin wani aiki. 

Aceawar kafar WebMD, hakan ya sanaya a lokacin bugun zuciya jinin dake zagayawa a zuciya yana raguwa da kuma sanaya jin gajiya a damtse.

 Don ka kare lafiyar ka ya zama wajibi kaje kaga likita ba tare da bata wani lokacin ba don ya duba lafiyar ka. 

2. Raguwa yin numfashi; Zaka dinga jin raguwar numfashin ka, alala misalai idan ka hau bene zaka dinga yin haki. In har kaji kana yin numfashi da qyar da jin gajiya bayan ka yi yar tafiya to wanana alamu ne na ka kamu da bugun zuciya. 

Acewar MayoClinic, zuciya tana taka rawa sosai wajen tura iska zuwa sassan jikin dan adam da kuma cirewa wasu sanadaran da jikin baya buqata. 

3. Jin zafi mai radadi a zuciya: Idan kana jin zafi mai radadi a zuciya wanda kuma bai cika damun ka ba, ka tabbatar da ka tuntubi likitan ka domin wannaa alamu ne na bugun zuciya kuma wannan alamar tana hana jinni yawo zuwa zuciya. 

4. Gurbacewar ciki: Bugun zuciya wani lokacin yakan janyo lalacewar ciki kamar jin amai,inda hakan ya kan faru ne saboda wani irin abinci da kaci. 

5. Fesowar quraje a baya ko a damtsen hannu ko a cikin qirji:

 Jin zafi a wadanan wurare alamomi ne na an kamu da bugun zuciya kuma hakan yana janyo rashin fitar iskasaboda jijiyon jinni sun rufe. Idan ka fara jin alamu ka tabbatar da kaje kaga likita.

 6. Jin rashin sukuni a maqogoro ko wuya ko a muqamuqi: A nan zaka dinga jin rashin sukuni a maqogwaraon ka ko a wuya ko kuma a muqamuqin ka wanda kuma baka taba jin irin sa a baya ba, haka mutane m,asu fama da ciwon siga, sukan mayar da hankali a dukkan wani chanji da suka ji a jikin su.

 7. Jin wani chanji gaba daya na ba dai dai ba a jiki: 

A koda yaushe ka dinga sauraron wata murya da zaga dinga ji a cikin kanka, wananna ana yi maka gargadi ne. Wasu marasa lafiya su kan gayawa wasu likitocin su cewar basa ji sosai a saboda haka ya kamata ka tuntubi likita in ka fara jin hakan.



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top