Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace amfani da na’urar tantance katin zabe ne sanadiyar nasararsa a zaben 2019

- Buhari ya kayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, a zaben Shugaban kasa

- Shugaban kasar yace Allah ne ya sa shi zama Shugaban kasa bayan yayi takarar kujerar sau hudu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa amfani da na’urar tantance katin zabe ne yayi sanadiyar nasararsa a zaben 2019, inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar.

Shugaban kasar wanda aka rantsar a karo na biyu, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Premium Times.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban kasar yace Allah ne ya sa shi zama Shugaban kasa bayan yayi takarar kujerar sau hudu.

Yace: “Da lokacin da Allah ya diban mun ya kai, yayi amfani da fasaha wajen shigar dani.

“Na’urar tantance katin zabe ya hana wadanda ke mulki rubuta sakamakon karya kamar yadda suka saba yi.”



Shugaban kasar yayi alkawarin ba wasu bangarori uku muhimmanci, wadanda suka hada da tsaro, tattalin arziki, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Yace zai tabbatar da samar da ayyukan yi, da kuma mayar da hankali wajen samar da wutar lantarki, kayayyakin more rayuwa, harkar lafiya, fasaha, da sabon tsari a fannin ilimi tare da mayar da hankali kan kimiya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top