Dayawan mutane na tambayar dalilin hana jariri ruwa na wasu watanni, hakan baya rasa nasaba da rashin sani kokuma fadakarwa akai.

 Bincike cewa kashi 80 cikin dari na Nono ruwa ne. Kaso ashirin ne abinci Wanda kuma ke dauke da sanadarai daban daban na lafiya kuzari da magani. Kuma ko shakuwa jariri yake aka ba shi ruwan nono zai daina. Kuma jariri ba kamar babba yake ba, wanda ya san ruwa kuma ya saba da shi, shi jariri bai san ruwa ba sai an saba masa da shi.
Dalilan da suka sa Hukumar Lafiya ta bullo da wannan dabara su ne na rage gudawa da tari a jarirai sanadiyyar kwayoyin cutar da ke cikin ruwan sha. 

Abin dai kwatantawa a nan a misali shi ne; ko yaron da aka ba nono zalla yana samun yawan matsalar gudawa da yawan tari ko ba ya samu? Sa’annan kuma a auna da wanda tun daga ranar da aka haife shi ake ba shi ruwa ko da tsabtatacce ne, a gani shi yana gudawar ko ba ya yi?

Amsar wannan tambaya a mafi yawan lokuta ita ce, shi jariri na farko yawanci bai cika samun laulayin gudawa da tari ba, ko da ya samu ma da sauki za su zo ba kamar mai shan ruwa ba.
Ban da ruwan nono, ai an yarda kuma a ba jariri ruwan gishiri da sukari idan yana gudawa, ko idan an rubuta masa wasu magunguna ko bitaman duka a ba shi. Kowa ya san ruwan gishiri da sukari da ruwa tsabtatacce ake hada shi. Ke nan a likitance dai ruwan shan sai idan uwa ta tabbatar fes yake, wato an tafasa shi ya huce kuma an zuba a kofin da shi ma tafasa shi ake a kullum. To rashin bin wannan ka’ida ne na tafashe-tafashen ruwa da kayan abincin jarirai, wanda ke da matukar wahala, ke sa hukumomi bullo da mafita irin wannan ta hana jarirai ruwa. Daga wata shida kuma sai a fara shan ruwan a fara dorawa da abinci kamar yadda wannan jadawali na Hukumar Lafiya ya kwatanta:
Watanni 6 zuwa 8: A fara da abincin da aka dama kamar kamu, cerelac, kunun gyada da sauransu.

Za a iya ci gaba da ba da abinci mai ruwa-ruwa kamar faten dankali sau 2 zuwa 3 a rana, gami da shayarwa, dangane da bukatar jaririnki.
A fara da karamin cokali biyu zuwa uku daga farko-farko. Sa’annan daga bisani a iya karawa.
Watanni 9 zuwa 11: Bayan irin mai ruwa-ruwa na sama, fara ba da sauran abinci mai kauri amma wanda aka mutsuke kamar kwai, naman kaza mai laushi da sauransu. A fara da kayan marmari ba ruwan juice ba sau 3 zuwa 4 a rana gami da shayarwa dangane da bukatar jariri. Rabin karamin kofi.
Watanni 12 zuwa 23: A wadannan watanni kusan za su iya cin duk wani abinci mai laushi ko da ba a mutsuka ba. Sau 3 zuwa 4 a rana gami da shayarwa daidai da bukatar jariri. 

Musani kula da jariri hakkine akan iyaye.

Allah yasa mudace Ameen


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top