🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿🧿

Bayanin kusan maimai ne domin nasha yinsa abaya. Ciwon Kai na ‘Migraine’ Yana daga cikin cutukan gado da suka fi addabar mata. Sai de wasu lokutan yakan addabi wasu daga cikin maza kalilan, amma dai mata ne suka fi zuwa mana da shi asibiti.

Ciwon kai ne mai tsanani mai zuwa kusan wata-wata kamar al’adar su matan. Yafi kama 6ari daya na kai, kuma mace zata rika jin alamu kafin yazo wadanda ke nuni da cewa ciwon ya kusa zuwa. 

WADANNAN ALAMU SUN HADA DA:

1- Rashin son haske 
3- Rashin son jin Qarar abu 
2- Ganin walkiya-walkiya da sauransu. 

A wasu lokutan kuma ba alamun sai dai kurum aji ciwon kan yazo lokaci guda 

Sauran alamun ciwon sun hada da yawan tashin zuciya, ko amai.

Matsalar bata cika tafiya da magungunan kashe zogi na Panadol ko ibuprofen ba. Dole sai anba mutum magunguna masu karfi, matsalar take lafawa musamman wadanda ke aiki a kwakwalwa wato mood stabilizers. Don haka idan mutum na fama da irin wannan matsanancin ciwon kai, dole sai yaje wurin kwararen likita ya rubuta masa magani mai karfi wanda kuma ya dace da yanayi

MEKE HADDASA CIWON

Shi ciwon har yanzu ba'a tantance me yake kawo shiba, amma an dai san yana bin zuri’a wato uwa takan sa wa ’yarta Ko ya'yansu dauka daga uba, ko kakanninsu.

Sauran abubuwan da aka danganta da matsalar sune shan kwayoyin rage haihuwa wato pills da samun juna biyu da tsayawar al’ada a mata idan sun manyanta. 

Sai triggers ma'ana akwai nau'in ire-iren abinci dakan tayar da ciwon wadanda su masu matsalar ya kamata su lura su guje musu. Sai kuma rashin samun isasshen hutu, yawan kallon screen walau na waya ko a tv, toshe kunnuwa da headphones na tsawon lokaci duk an tabbatar suna sa saurin tashin ciwon.

ILLAR YIN WATSI DASHI

Likitoci na gargadi akan ya kamata mai ciwon ya rika ziyartar asibiti kada yake shan magungunan rage zogi agida kurum ya basar da ciwon domin migraine na iya haddasa abunda ake kira MIGRAINOUS INFARCTION Wanda ke haddasa strokes wanda hakan kan jawo shanyewar barin jiki koda mutum baida hawan jini saboda mutuwar kwayoyin halittun kwakwalwa na gun da abun ya faru.

MATAKI

Kafin akai ga likita a iya shan pracetamol, asami ruwan dumi adaddana sashin kan wato tausa, a kashe hasken daki akwanta mutum ya saki jiki ya samu relax, sannan aje gq likita.
.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top