πππππππππππππππππ
Na kara nazarine kan sauya tunanin mu zuwa kan Wannan ciwo da ake ganin kamar bashi da illa.
Shide Ciwon Hanta:- Wasu kwayoyin cutar birus ne ke shiga cikin hanta ta hanyar jini ko ta baki su kawo ciwon.
Akwai nau’insu har kusan kala shida:--
1- akwai ajin A,
2- akwai B,
3- akwai C,
4- da D
5- da E
6- da kuma F.
Amma anfi ganin nau’uka uku na farko wato A, B, da C. acikin wadannan ukun ma anfi ganin rukunin ko ajin B, wanda kuma shine yafi yiwa hanta illa duk da C ma ba kanwar lasa bane. Ya kamata asan banda wadannan rukunin kwayoyin cuta akwai sauran abubuwan da suke kashe hanta, kamar giya da burkutu da shan miyagun kwayoyi da shan wasu guba irin wadanda mahaka kuza suke samu kamar gubar karafuna irinsu dalma (arsenic, metallic, leads poisons) da sauransu.
Rukunin B_ &_ C
Nau’in da zanyi magana akai sune wadanda kwayoyin cutar rukunin B da C ke kawowa. Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta masu nakasa hanta hanyoyi daya ne da ake daukar cutar kanjamau wato ta hanyar jini.
A yanzu haka anfi samun mace-mace daga cututtukan hanta fiye da mace-macen cutar kanjamau saboda ba'a samun magungunan ciwon hantar kamar yadda aka samar dana kanjamau, haka nan kuma saboda fadakarwa da ake tayi akan ciwon kanjamau din ana mantawa dana hanta.
Domin a yanzu mutane fiye da miliyan daya da dubu dari bakwai ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta, yayin da masu kanjamau miliyan 1 da dubu dari uku ne ke mutuwa a duk shekara.
Haka kuma kusan kowa yasan cutar kanjamau amma da yawa basu san ciwon kumburin hanta ba. Shiyasa da yawa mutane idan zasu yi aure sai dai ayi gwajin kanjamau kawai ba a hadawa dana hepatitis. Yawanci a wurin gwajin bada jini kawai akan gano mutum yana dauke da cutar. Tunda sai tayi shekara da shekaru mutum baima san yana dauke da kwayar cutar ba.
HANYOYIN KAMUWA
Hanyoyin da ake daukar kwayoyin sune;
A- Yayin saduwa daga mai dauke da kwayar zuwa wanda bai dauke da ita.
B- Sai kuma ta hanyar karin jinin da ba a yi wa gwajin tantance kwayar cutar ba.
C- Sai kuma ta hanyar amfani da kayan kaifin da ba su da tsabta, kamar askar wanzamin da ba a gasa ba, amfani da rezar da mai ciwon ya yi amfani da ita, ko amfani da allurar da aka yi wa wani, maimakon sabuwa.
D- Sai ta hanyar cin abinci da cokali daya tare da maicutar, ko ya gwaguiyi Abu da baki ya baka kaima ka dora wato idan miyau ya hadu kenan
E- Wata hanyar kuma ta daukar ciwon a yara itace ta wurin uwa mai kwayar cutar, yayin haihuwa ko yayin shayarwa.
Da yake kwayoyin cutar shiga cikin hanta suke suyi barcinsu, da yawa masu dauke da kwayoyin basa jin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da kwayoyin suka farka suka fara cin hantar sa’annan alamu zasu bayyana. Wannan na faruwa ne kawai a kashi daya 1% cikin hudu na wadanda ke dauke da kwayar, sauran kashi ukun ba za su taba nuna wata alama ba duk tsawon rayuwarsu, shiyasa aka fi cewa masu dauke da kwayar su kwantar da hankalinsu domin zai wahala su nuna alamun. Amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.
ALAMOMIN CIWON HANTA
1- Yawan zazzabi,
2- Yawan ciwon ciki bangaren dama,
3- Yawan tashin zuciya da rashin son abinci,
4- Yawan kasala
5- Idan tai kamari akan iya ganin kumburi a fuska da kafafu
6- Yawan samun shawara, wato kadawar ido zuwa ruwan dorawa da sauran alamu da mutum zai ji dai cewa ba lafiya ba.
A daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin kashe kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya, wanda babban abin da suke kawowa shine motsewar hanta ko ciwon daji na hanta. Magunguna da alluran da ake amfani dasu aci karfin kwayoyin cutar kafin su kai ga illa suna da matukar tsada sosai, shi yasa mukan ce riga-kafi yafi magani.
HANYOYIN KARIYA
1- Kamewa har sai anyi aure, masu auren ma su rike matansu kawai.
2- Tabbatar da an yi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure, da nuna wa juna takardar shaida kafin a daura auren.
3- Tabbatarwa cewa jinin da za'a kara wa mutum angwada shi a asibiti an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cuta.
4- A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon. Idan an samu mace mai kwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi.
5- A yanzu akwai alluran riga-kafin kamuwa daga wadannan kwayoyin wadanda aka sa a rika yi wa yara da zarar an haife su, sa’annan a watanni na biyu da na uku, akasin kwayar kanjamau wadda har yanzu ba a gano allurar riga-kafinta ba.
SAURAN HANYOYIN SUN HADA DA;-
6- Ba yara kawai ba har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za a iya yiwa allurar riga-kafin.
Wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya, musamman masu aiki a dakin gwajin jini, mata masu zaman kansu da mutanen da ke aiki cikin damara. A ma’aurata wadanda daya ke da kwayar cutar amma daya ba shi da shi, shi wanda ba ya dauke da kwayar cutar sai a yi masa riga-kafi. Ana samun wadannan allurai a asibitocin da mata ke zuwa awo.
7- A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko a kona su da wutar lighter ko a wanke su da sinadarin bleach kafin a yi wa mutum amfani da su. Sai dai idan sabuwa ce daga ledarta aka bare a gaban mutum. Haka ma sirinji da reza, a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani dasu.
8- Zuwa cibiyoyin gwaji na kyauta don sanin matsayin mutum na taimaka wa rage yada ciwon.
ALLAH KASA MU GAMA LAFIYA AMIN
Barka da shan ruwa
(Ibrahim Y. Yusuf)
© Sirrinrikemiji
Post a Comment