πππππππππππππππππ
Akwai tarin abubuwa da rashin sani ko sakaci kan kai ga aikatasu kan shafi rayuwar abunda ke cikin masu juna biyu wato (pregnant mothers) batare da ansani ba inda karshe hakan kesa ahaifo yaron dazai zo iyaye na shan wahala wajen magani koma kyamarsa cikin alumma. Ko aje ana neman milyoyi ana za'aima yaro aiki. Daga ciki akwai haihuwar yaro da ido daya wajen goshi, tsagaggen lebe, hannuwa hudu, jarirai ciki ahade, da karamin kai.
Daga ciki akwai Yin sabon fenti agidan da yake akwai mace mai juna biyu na kasa da wata hudu na daga cikin abunda ke jawo haihuwar yara da nakasa wato congenital anomalies kama daga budadden gadon baya, haihuwar da tsagaggen lebe, ko rashin wani sashi na jikinsu musamman ma yaran da ake haifarsu babu kuzari kamar wadanda aka durama guba.
Haka ma koda fentin ba ajikin gini yake ba, in mace na taammali da yawan shakarsa hakan na iya faruwa.
Sannan kwankwashe tsohon gini da yi masa kwaskwarima a canza fenti shima shike jawo guba jikin kananun yara abunda muke kira LEAD POISONING aga yara na seizure kamar masu farfadiya, ko gasu a zaune ko atsaye amma aita magana batare da anji sun mayar ba azaci ko iskanci ne kurum, wani lokacin harda yawan amai.
Don haka fenti de guba ne ga mai yaron ciki da kuma kananun yara inya zamto ajikin tsohon gini akayisa saboda chemicals. Amma mai ciki basai tsohon gini ba, koma wanne iri ne ai hakuri da shafawa sai bayan ciki ya tsufa ko ankusa haihuwa.
Amma amarya wannan wanda dama anyi fenti sai yanzu da tazo cikin zai shiga akwai a iya cewa akwai saukin hatsari tunda sannan karfin chemicals din ya ragu a iska, amma de anaso dole ga duk wadanda suka shirya daukar ciki koma suka sami cikin su maida hankali wajen shan FOLATE da Vit B da akam basu domin suna rage hatsarin haihuwar ya'ya masu nakasa 200% bama 100% inji kwararrun masana. Yayin da fenti keda 200% chance na haddasa illa ga yaro wacce koda ba aganta azahiri ba to a muamalarsa inya fara girma zata nuna.
Sai zukar hayakin taba, da kaucewa shan magunguna barkatai ciki kuwa harda na gargajiya suna taimakawa sosai.
Wannan tasa ba ason karya inmace tasan tana da ciki ko likita bai tambaya ba tai masa bayani saboda wasu magungunan na iya ratsa cikin mahaifa suima yaro illa musamman irinsu: Ja da yellow wato tetracycline, vitamin A, thalidomide, Phenytoin, da duk sauran magunguna dake da tasiri a kwakwalwa.
Wannan fadakarwa mata akaima amma batun fenti musamman da maza nake domin mune keda alhakin wannan. Amma sauran na mace ne in kunne yaji jiki ya tsira.
Allah sa agama haife haife lafiya amin.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment