Suna: Girman Kwabo
Tsara Labari: Malam Zaks
Kamfani: Sun Shine Mobies
Shiryawa: Tasi’u Yusuf Ayagi
Umarni: Hamisu Yusuf Ayagi
Jarumai: Bashir Nayaya, Rabi’u Rikadawa, Alasan kwalle, Inuwa iliyasu, Isyaku jalingo, Aliyu Rara, Ayatullahi Tage, Jibril Laku-laku, Fatima A. Gombe, Raihan Katsina, Rukayya Mohd, Fiddausi I. Abdullahi, Zainab Y. Abdullahi.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Alhaji Shuhu(Bashir Nayaya) a zaune a gidan sa ya cire hular kan sa ya fito da kudi zai kirga, babu zato sai matar sa ta fito daga cikin daki ta gansa, hakan ya sanya shi sake boye kudin yana yi mata fada akan fitowar ta har ma ta tambaye shi kudin siyan gishiri ya hana ta. An nuna Alhaji Shehu a matsayin mutum mai arziki amma wanda kudin sa basa ciwuwa, ba ya son taimakon mabukaci indai ba yasan cewa zai amfana da mutum ba, domin akwai inda Liman yazo neman taimakon kudin siyan ‘loud speaker’ ta masallaci ya hana shi domin yana ganin hakan ba abu ne da zai ci riba ko kuma ya links kudin sa da zai bayar ba.

A wani bangaren kuma an nuna Idris (Isyaku Jalingo) yana zaune da matarshi wadda suke zama irin na so da kaunar, saidai kuma rashin lafiyar da ya kama matar tashi hakan yasa za’a yi mata aiki, amma bashi da kudin da zai biya don yiwa Matar tashi aiki, kasancewar shi mutum mai rangwamen karfi ganin kuma babu hanyar da zai samu kudin yiwa matar tashi aiki sai yaje neman rancen kudi wajen Alhaji Shehu amma sai Alhaji yaki amincewa da ya bashi kudin kai tsaye ba tare da an bashi jinginar wani abun ba, hakan yasa Alhaji Shehu ya bukaci Idris ya kawo masa takardun gidan sa kafin ya bashi kudin.

Shi kuma Idris ganin babu yadda zai yi bashi da wani dabi wanda yafi amincewa da bukatar Alhaji Shehu, dole tasa yaje ya kawo masa takardun gidan nashi, sannan Alhaji ya bashi kudin da za’a yiwa mayar tashi aiki, bayan wasu lokuta Alhaji Shehu ya bibiyi Idris akan yana bukatar kudin sa ko a fita a bar masa gida, rigima ta kaure a tsakanin su wadda har takai su gaban hukuma, Idris da iyalan sa suka bar gidan aka kulle.
Daga bisani sai Alhaji Shehu ya tsiro da dabi’ar karbar kudi a hannun samarin da suke zuwa hira wajen ‘ya’yan sa ‘yan mata, domin ya kasance mutum ne shi me kwadayin abin duniya kuma bai damu da kallon rashin da cewar hakan da wasu za suyi mishi ba, da tafiyar ta cigaba a haka kuma sai ya zamana cewa har takai cewa da sanin shi samarin kan fita yawon shakatawa da ‘ya’yan shi kuma dalilin hakan yasa daya cikin ‘ya’yan nasa tayi cikin shege. Amma duk da faruwar hakan bai saduda ya gyara halin shi ba.
Daga karshe kuma wasu ‘yan damfara suka zo wajen Alhaji Shehu da tayin kasuwancin da zai zuba jari wanda zai samu kudi fiye da adadin abinda ya zuba a cikin kasuwancin, bayan sun yi masa dadin baki sai ya amince dasu kuma ya kwashi dukiyar sh ya basu suka tafi don yin kasuwanci, tun daga sannan aka talauta Alhaji ya wayi gari bashi da komai.

Abubuwan Birgewa:

1- Sunan fim din ya dace da labarin.
2- Jaruman sunyi kokarin bawa mai kallo dariya ta hanyar yin barkwanci.
3- Marubucin yayi kokari wajen ganin labarin ya rubutu ta sigar data dace.
4- An samar da wuraren da suka dace da labarin.
5- Hoto ya fita radau, sauti ma ba laifi.

Kurakurai:

1- Bayan jami’an tsaro sun kulle gidan Idris akan bai biya Alhaji Shehu kudin sa ba, an nuna Alhaji Sule yaje wajen Idris yayi masa alkawarin zai biya masa bashin makudan kudin da ake bin sa, kuma zai bashi aron gida su zauna da iyalin sa, tare da nema masa babban aikin yi a kasuwa. Shin wanene Alhaji Sule da yayiwa Idris halacci haka? Ya dace a nuna alakar dake tsananin sa da Idris, kamar ta ‘yan uwan taka ko ta abota da sauran su.
2- An nuna Rabi’u Rikadawa a matsayin mafarauci kuma sarkin dawa. Amma yanayin maganar da aka nuna yana yi bata yi kama da ta mafarauta ba, tafi kama da ta kauraye ko rikakkun ‘yan daba.
3- Lokacin da rabi’u rikadawa suke sallama da matar sa da dansa (Ayatullahi Tage) akan zai koma daji farauta, maganar su bata hau da bakin su ba, tashin muryar su daban kuma yanayin motsin bakin su daban. An samu irin wannan matsalar ta rashin hawan murya da bakin jarumai a cikin sina sinai da yawa.
4- An nuna ‘yar Alhaji Shehu tayi cikin shege amma bamuga matakin da Alhaji Shehu ya dauka a kanta ko a kan wanda yayi mata cikin ba, duk da kasancewar irin wannan matsalar ta zama abu mai girma a al’adar bahaushe. Ya dace Alhaji ya dau mataki musamman akan mutimin da yayiwa ‘yar sa ciki.

Karkarewa:

Labarin ya nishadantar, kuma an tabo wani bangare na wasu matsaloli wanda suke faruwa a cikin al’umma. Sai dai kuma zaren labarin bai dire har karshen sa ba ta yadda zai gamsar da mai kallo. Wallahu a’alamu!

®LLeadershipayau.ng

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top