⛔⛔⛔⛔⛔♨♨♨♨♨♨♨⛔⛔⛔⛔⛔

Aikata wadannan dabi'un marasa kyau ga mutum na iya jawo mai ciwon koda (Nephritis) don haka inkaji ko kinji wani Abu da kinsan halinka ne to ka daina.

1] RIKON FITSARI

Jinkiri wajen yin fitsari cutar da Kaine mutum ya kasance yanajin fitsari amma yaki zuwa yayi yaita rikon sa yana takurewa, to ku Sani duk sanda koda ta tace fitsari ta turo shi ga mafitsara ba abunda da akeso irin afitar dashi domin inkana rikeshi to ahankali wani zai fara komawa ga koda (kidney) wanda daga nan kuma matsala zata fara afkuwa.

2] KIN SHAN ISASHSHEN RUWA

Rashin shan ruwa wadatacce yadda ya kamata nan ma matsala ne yazama mutum yana jin kishi sai yasha kadan ko kuwa ma mutum ya gama cin abinci musamman mai maiko amma yaki shan ruwan kwata-kwata haka musamman abinci mai nauyi da mai Gina jiki irinsu (carbohydrate & protein). Mai irin wannan hali ya Kuka da kansa shi ruwa anso kake shan sa basai in kana jin kishi ba 

Sannan inda hali in abinci ka gama ci to kasha ruwan mai dumi, kona tea ba ruwan sanyi ba. Inko na sanyi ne toh saika gama cin abincin da kamar minti 10 tukun

3] YAWAN SHAN GISHIRI

Yawan shan gishiri akwai matsala ga koda basai ga mai hawan jini ba, musamman mutanen dake da irin dabi'ar nan ta karama abinci ko Miya danyen gishiri idan bai musu daidai ba, to suma su kiyaye yana interfering da aikin cortex cikin koda.

4)] SHAN MAGUNGUNA

Rashin daukar kananun cututtka ko symptoms da mahimmanci wanda mutum ke ganin ko ba'a sha magani ba xa'a warke kamar jin zafin kuibin cikin wajen gadon baya ko murdawar ciki, zafin fitsari ko kaikayin makogoro ko ciwon mara yayin alada. Ta yadda mutum shine likitan kansa saide yaita dannawa jikinsa su paracetamol da feldin daka.

Sannan kuma shan magungunan ba bisa kaida ba, kuma ba yadda likita ya tsara ba, da kuma wanda dama ba likitan bane yasa wato (self medication) wannan na cutar da koda kwarai da gaske don haka duk mai irin wannan Shima to ya Sani ya mikawa Ciwon koda takardar gayyata. 

Sannan kananun jami'an lfy wani lokacin kuna taimakawa wannan barnar mutum baisan pharmacotherapeutic na drugs ba kurum symptoms din da yake kawarwa ya sani amma sai yaita rubutawa marasa lfy batare da daukar koda history na sauran cuttukan dake zama contraindications na drugs. Kuji tsoron Allah in ba ai training dinka kan haka ba kabar aikin ga masu shi.

5] YAWAN CIN NAMA

Yawan cin Nama fiye da ka'ida. Suma masu wannan al'adar su sani cewa ba burgewa bane ace kamai da cin Nama kullum kullum ko kuwa kwana 1 ko 2 kurum kake daga kafa, hasali ma Kila baka ko baki da kokarin motsa jiki, Sannan inkuka samu sai kunji kunci kunyi hani'an to mutum lallai ya kiyayi kansa.

6] QWAURON ABINCI
Rashin cin wadataccen abinci, mutum ya rika ma kansa kwauro da gangan Saboda tsurfa ko kuwa tunanin kar yai kiba, to masu irin wannan suma su kula.

SHAWARA TA AGAREKU

Shifa jiki yanason service kamar Mota ce in ana mata juye tafi lafiya. Don haka jiki ma na bukatar hutu, wanka, sanya tsaftataccen tufafi da kuma abinci mai kyau ba mai tsada ba. Yana da kyau karka maida cikin ka koda yaushe abinci iri guda wato kaita cin carbohydrate ko protein wlh jiki bayason haka shyasa masu yawan cin carbohydrate kanyi fama da kitse ajika haka suma masu cin protein kanyi ta fama da nauyin jiki.

Kasani inkana cin wadannan (masara, tuwo, dankali, doya, rogo, garin kwaki, flower,) koda ba rana daya kake hadasu ba Kaci wlh Abu daya kake ci kullum domin duk carbohydrate ne, don haka ake gaurayawa da vitamins, lipids, water, protein, and minerals ai tsari me kyau.

Ake fita fitsari Akan kari da anji alamunsa

Da anga Alamun cuttukan sanyi wato kaikayin gaba, ko fitar ruwa agaba ga mace ko namiji anemi magani ku dena yadda da zancen cewa ko ba magani yana tafiya ko kaji wasu ma ana cemusu wai mataccen maniyyi ne, duk karya ce bawani mataccen maniyyi a likitan ce.

KARSHE DA ANJI ALAMUN:

▶Yawan ciwon baya daga kasa ko sama wajen kafada,
▶Canzawar dandanon baki zuwa kalar kanwa ko karfen da yai tsatsa,
▶Canzawar fitsari xuwa duhu duhu kuma kadan kadan in anje yi,
▶Yawan ganin jiri da kasa samun nutsuwa,
▶Yawan kasala,
To ahanzarta zuwa aga likita domin wadannan Alamun Ciwon ne.

Allah ya karemu! Ya karamana lfy da zama lafiya.

(Ibrahim Y. Yusuf)


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top