Daya daga cikin jaruman fina finan kannywood wanda ya dade ya na taka muhimmiyar rawa a masana’antar ya bayyana cewa rashin sanin ciwon kai da rashin girmama juna a Kannywood a matsayin abubuwan da su ka fi komai ci mai tuwo a kwarya. Yadda kowa ya ke da ‘yancin yin abinda ya ga dama ba tare da tunanin wanda ya ke sama da shi ba.jaridar blog.Northflix.ng na ruwaito

Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da su ke tattaunawa da wakilinmu, inda ya ke tambayarsa me ya ke ganin ya na kawo yawan cecekucen da baya karewa a masana’antar kannywood.

Baballe ya bayyana cewa “Rashin hakuri na rayuwa da kuma rashin daraja juna, duk masana’antar duniya ana samun irin wannan matsalar amma ina ganin namu ya fi yawa, kuma duk sakamakon rashin sanin mutuncin juna ne”

Jarumin ya ce “ita rayuwa 'zo mu zauna zo mu saba ce, sai dai kuma idan ka na da matsala da mutum bai kamata a ce ka yayata shi a duniya da sai kowa ya sa ni ba, gara ka nemi mutum ku yi iya ku yaku.

Yawan yada korafe korafe a soshiyal midiya ba komai ba ne face tonan asiri ga junan mu. A ganina gara mu yi ta a tsakanin mu ba tare da kowa ya sa ni ba. Kamar yadda na fada a baya ita rayuwa zo mu zauna zo mu saba ce. Don haka rashin sanin ciwon kai da rashin mutunta juna da kuma rashin hakuri shike jawo mana wannan matsalar.”

 Idan har zamu gyara wadannan abubuwan guda biyu yaro ya girmama babba, babba kuma ya girmama na kasa da shi saboda wanzar da zaman lafiya ga junan mu. Toh duk wadan nan abubuwan za su wuce a masana’antar mu kuma mu samu zaman lafiya ga junan mu.” A cewar Baballe Hayatu

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top