JARIDAR DIMOKURADIYYA: Da alama fa Jarumar masaantar shirya Fina-Finan Hausa na Kannywood, Rahma Sadau, ta hasala don har ta fara zuzzuga Ashariya ga mabiyan ta na shafin Twitter.

Tun bayan bulla wadan su sababbin Hotuna dake bayyana wadan su bangare daga cikin bangarorin da Addini ya hana Mata su bayyana Jarumar ke shan suka musamman daga wajen Musulman duniya.

Wato Jarumar tayi shigar ne a Jihar Kaduna a lokacin bikin bude tankameme dakin cin Abinci mallakin kan ta.

Martanin Mutane kan shigar da tayi yasa ita ma ta fara dura Ashariya tare da ikirarin dun Wanda ya fasa.

Har ila yau Jarumar ta bayyana cewa baa yin Nasiha a bainar Jamaa.

Kazalika ta ce rashin aikin yi shine yake saka mutane shiga shirgin daba nasu ba suyi ta surutu a kan abun da bai kai ya kawo ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

  1. Slm rahahama yar gatan kd bakiyanki fadawanki up up rahama sadau allah yasareki

    ReplyDelete

 
Top