Kowannen mu ya san muhimmancin da ruwa ke da shi wajen tabbatar da kasancewar mu cikin koshin lafiya, toh sai dai da yawa ba su san adadin ruwan da ya kamata su na sha ba.

Ko a tsakanin masana, babu daidaito a ra’ayoyin su game da wannan. Yayin da wasu ke ganin kofi 8 a rana ya wadatar, wasu suna ganin mutum na bukatar akalla lita 3 a rana.

Koma ya ya ne dai, jikin mutum kan yi masa nuni idan yana bukatar ruwa ta hanyar jin kishi, bushewar baki, jiri da sauransu. Kuma akwai matukar hatsari idan mutum ya ki la’akari da wadannan alamomi.

Akwai illoli da dama da rashin shan ruwa isasshe ke haifarwa, Kadan daga cikin su sun hada da:

1. Tamushewar fata da saurin tsufa

Related image

2. Rashin iya narka da abincin da aka ci da wahala wajen fitar da bahaya

Related image

3. Gyambon ciki

Related image

4. Rama

Related image

5. Ciwon gabobi

Related image

6. Zafin jiki

7. Mantuwa da toshewar kwakwalwa

8. Rashin kuzari da saurin gajiya

Da sauransu.

Da fatan za a jimiri shan ruwa domin ganin an gujewa wadannan Illoli.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top