img ©Hmini

Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola ta bayyana cewa babu wani tasiri da Fina-finan Indiya zai yi kan fina-finan Kannywood duk da ko sun bade kasuwani.

Teema tace dama can tun tana karama burinta shine taga kanta a farfajiyar fina-finan Hausa sai gashi kuma Allah ya cika mata Buri.

Teema ta fadi haka da wasu ababe da dama a hira da tayi da PREMIUM TIMES a garin Kaduna.

” Tun ina yar’ karama nake burin wata rana in ganni a farfajiyar fina-finai, toh kuma sai gashi a kwana – atashi Allah ya cika mini burina na sami kai na a farfajiyar Kannywood.

” Zuwa yanzu na fito a fina-finai da dama. Wadanda nake muradin su kuwa sune Tsagegeduwa, Mugun Zama da Tozarci.

Teema tace a tsawon shekarunta da fara fina-finai, bata taba yin koda cacan-baki ba ne da wata ba ko wani Forodusa, ko Darekta. Tace kowa takan dauke shi dan uwanta ne.

Da aka tambaye ta ko rashin fitowar fim a kasuwanni yanzu zai iya kawo wa masu shirya fim din wani matsala sai tace ”
Babu wani matsala da hakan zai yi. Sinima ake fara nunawa inda bayan an nuna a nan sai kuma a sake shi a kasuwa. Ni banga wani matsala da yake kawo wa ba.

” A harka ta babu matsala kuma ba zai shafi shanawar tauraro na ba.”

Bayan nan Teema ta yabi wasu daga cikin abokanan aikin ta kamar Fati Su, inda ta kurantata da cewa macece mai kamar maza.

” Duk da cewa kowa nawa ne a farfajiyar Kannywood. Salin Alin, muna mutunci sannan lafiya-lafiya muke da kowa, amma Fati SU ta shiga min rai. Tana da Hakuri da tausayi ga kuma dattaku. Wadannan halaye nata ya sa take burgeni. Sannan ina da wasu kawayen da duk abokanan aiki na dole in yaba musu. Kannywood a wurina tsintsiya ce madaurinta daya.

Post a Comment

 
Top