Kamar da yadda muka karanta a baya cewar akwai wasu haƙƙoƙin da maigida ke da su akan uwargida tun daga lokacin da ta samu juna biyu har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya, haka kuma akwai haƙƙoƙi a kansa bayan an sauka lafiya. Kaɗ an daga cikin su sun haɗ a da:

(a) Isasshen abinci 
(b) Kula
(c) taimako/hutu

Babban abin da ya kamata ya biyo baya; bayan uwargida ta sauka lafiya, shi ne samun Isasshen abinci: Yana ɗ aya daga cikin haƙƙin maigida ya tabbatar ya yi tanajin isasshen abinci domin ciyar da maijego. Saboda a wannan lokacin tana bukatar abinci daban-daban da za su ƙara mata jini da lafiya a jikinta, ta yadda abin da aka Haifa zai/za ta samu nono ingantacce/lafiyayye kuma isasshe. A wannan lokaci akwai wasu abobuwa da Malam Bahaushe kan ba mahimmanci sosai, kamar yawan cin nama, kaji ko ganda domin ganin hakan zai sa uwargida ta maida jinin da ta zubar ta kuma samu ƙarfin kula da abin da aka haifa.

Uwargida ba an ce dole sai maigida ya siyo miki kaji ko nama kullum ba, a’a daidai abin da Allah yah hore muku za ku yi, idan ma babu halin sayen su ba komi sai maigida ya tabbatar cewa akwai isasshen hatsi da za a dafa uwargida ta ƙoshi.


Wani abu da aka ba mahimmanci a al’ada shi ne shan kunun kanwa wanda da yawa sun yarda cewar yana ƙara wa maijego ruwan mama (nono) domin shayar da jariri/jaririya. Don haka maigida ya yi ƙoƙarin tanadar gero ko dawa ko masara domin samar da kunun maijego.

KULA: Dole ne maigida ya kula da kuma sa ido a kan lafiyar uwa da kuma abin da aka Haifa. Haka na yiwuwa ta hanyoyi da dama –Maigida ya tabbatar ya ba uwargida fuskar sanar da shi dukkan canjin da ta ta ji da kuma wanda za ta iya gani tare da jariri/jaririya, shi ma ya riƙa kula domin sanin yanayin da uwargida ke ciki ta hanyar yi mata tambayoyi a-kai-a-kai irin su:
Idan an samu jariri/jarriya mai rigima( kuka) kuma musamman da dare kar maigida ya fusata, ya yi haƙuri kuma ya taya uwargida yin lallashi.

Taimako/Hutu: Maigida na iya samun lokaci na musamman da zai ba uwargida domin ta huta, misali idan akwai wasu yaran zai iya keɓ e lokaci na musamman da zai zauna da su ya riƙa musu tambayoyi da suka shafi addini ko kuma darusan da suka koya a makaranta tare da taimakawa wajen aikin gida da suke dawo da shi daga makaranta (homework). Waɗ annan abubuwa ne da za su gyara mana tarbiyar ‘ya’yanmu su kuma ƙara cusa soyayya da ƙauna a tsakaninmu da su.
Kodayake, wasu suna ganin sakewa da kuma taimakawa mace da hidimar gida wani abu ne da zai iya kawo raini. A’a, wannan ya danganta da yadda maigida ya bayar da kansa da kuma yadda ya tafiyar da gidansa (Asan cewar hakki ne akan iyaye wato uwa da uba su ba ‘ya’yansu tarbiya na gari, amma ba a bar uwa ita kaɗ ai tana fama ba).

Ya Allah ka yi mana jagora tare da ba mu zuri’a ɗ ayyiba amin summa amin.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top