Daga Bashir Sharfadi

Cikin wata sanarwa da aka rabawa maneman labarai a yau mai dauke da sa hannun kwamishinan ‘yansanda na jihar Kano CP. Ahmed Iliyas ta hannun kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ta bayyana irin yadda rundunar ta samu gagaruman nasarori wajen yaki da masa satar mutane don neman kudin fansa.

Sanarwar tace a ranar 12 ga watan Satumban da ya gabata ‘yansanda sun samu nasarar cafke wadansu mutane da suka hada da Paule Owne, da wata mai suna Mercy Paul Alias masu shekaru 38 mazaunan unguwar Dakata wadanda ake zargi da satar mutane.

An cafke wadanda ake zargin ne a yayin da suke kokarin tafiya da daya daga cikin yaran da suka sace mai suna Haruna Sagir Bako zuwa garin Onitsha na jihar Anambra.

Sun sace yaron ne a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata a yayin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya a unguwar ‘Yankaba.

Tun da farko dai mahaifin yaran mai suna Sagir Muhammad Bako ne ya sanar da ‘yansanda cewa bai ga ‘ya’yan sa ba, masu shekaru 2 zuwa 6.

Sashen binciken ‘yansanda na musamman da yaki da mugayen laifuka wato Operation Puff-Adder da hadin gwiwar sashen dake yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa, ya bi diddigi kan wadanda ake zargin.

Inda bincike ya gano cewa wadanda ake zargi sun jima suna satar mutane a unguwannin Sauna, Kwanar Jaba, Kawo, Hotoro, ‘Yankaba da kuma unguwar Dakata.

Binciken bai tsaya nan ba ya fadada har jihar Anambra, domin kuwa a ranar 13 zuwa 17 ga watan Satumban da ya gabata, ‘yansanda sunyi nasarar tseratar da sauran yaran da aka sace daga Kano a can jihar ta Anambra, bayan da barayin suka siyar dasu, wadanda suka hada da:

1. Umar Faruq Ibrahim mai shekaru 10 wanda aka canja masa suna zuwa Onyedika Ogbodo.

2. Aisha Moh’d Abdullahi ‘yar shekaru 9 wadda aka canja mata suna zuwa Ozioma Ogbodo.

3. Usman Mohammed mai shekaru 5.

4. Amira Auwal dan shekaru 4.

5. Husna Salisu ‘yar shekaru 4.

6. Blessing Ogbodo ‘yar shekaru 10.

7. Chiazozie Ogbodo dan shekaru 11.

8. Chiemerie Ogbodo mai shekaru.

Karin mutanen da ‘yansanda suka cafke kan satar da kuma sayar da yaran sun hada da:

Emmanuel Igwe dan shekaru 34 wanda ya taimakawa masu satar mutanen sai kuma Ebere Ogbodo da wata mata louisa Daru masu shekaru 45 sune dillalan da suka siya suka kuma siyar da yaran.

Sai wata mata Monica Orachaa mai shekaru 50 da suke siyarwa da yaran idan sun sato.
A wani bangaren kuwa a ranar 25 ga watan Satumban da ya gabata wani mutum mai suna Buhari Rabi’u mazaunin unguwar Medile a Kano.

Sai kuma Mubarak Gidare mai shekaru 23 dan karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.
Tun da farko sun nemi a biyasu kudin fansar yaron har N160,000 inda aka basu hakan.
Sai dai ‘yansanda sun samu kwato N124,700.

Tuni dai ‘yansandan jihar Kano ke kara kiran al’umma kan su cigaba da basu hadin kai domin yaki da bata gari.

Inda hukumar ke kara neman al’umma da su rika sanar da ita kan duk wani abu da basu gamsu dashi ba, domin dai a gudu tare a kuma tsira tare.





Allah ya kara taimakon jami’an tsaron mu, wajen kare rayuka da dukiyoyin mu amin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top